Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Mace mai shekara 65 ta haifi yarinya a Abuja

Wata mata mai shekara 65, Uwargida Comfort Timothy ta haifi jaririya mai koshin lafiya, bayan ta shekara 18 da aure ba ta samu haihuwa ba.

Aminiya ta binciko cewa Madam Comfort ta yi auren fari ne tun a shekarar 2001 amma bat a samu haihuwa ba, duk da cewa bat a saduda ba, ta yi ta addu’a tare da azumi a kai-a kai, domin Allah Ya ba ta haihuwa.

ADVERTISEMENT

“Na share shekaru masu yawa ina yin addu’a da azumi, ina rokon Allah, sai ga shi a yanzu Ya albarkace mu da haihuwar yarinya. Wannan nufin Allah ne kuma shi ya san dalilin da ya jinkirta har zuwa yanzu, domin ba mu taba karaya ba cewa Allah zai amsa addu’armu,” inji ta.

Ta ce ta shiga damuwa mai yawa kuma ta fuskanci kalubale mai yawa, “amma duk da haka ban karaya ba, domin na san komai dadewa zan samu biyan bukata, kuma ga shi a yanzu muna murnar samun albarkar haihuwa ta farko bayan aurenmu da shekaru masu yawa.”

ADVERTISEMENT

Aminiya ta gana da mijin matar, wanda yake cikin murmushi da farin ciki, ya ce wannan yarinya da suka haifa, ta kasance abin al’ajabi daga Allah kuma yana godiya ga Allah da Ya albarkace su da samunta.

“Mun dade muna addu’a kuma muna da yakinin cewa wata rana Allah zai amsa mana addu’a,” inji shi.

Iyayen jaririyar sun sanya mata suna “Ayobami” wanda haka ke nufin “Farin Ciki Ya Zo.” Sun shawarci sauran magidanta da ke fuskantar rashin haihuwa da su karfafa imani da Allah kuma su ci gaba da addu’a ba gajiyawa.

“Kodayaushe Allah na nuna ayarSa, don haka ina son mutane su yi imani da cewa sakon Allah gaskiya ne. Domin mu dai ba mu yi wani abu bad a ya wuce azumi da addu’a kuma ga shi a yau Allah Ya amsa mana.

“Watakila Allah Ya yi amfani da mu ne domin mu zama misali ga wasu, domin su ga karfin ikon Allah, cewa zai iya biyan bukatar bayinSa da suka yi imani da Shi,” inji shi.