Macizai na neman mamaye dakin gwaje-gwaje na Asibitin Gambo Sawaba

Shugaban Asibitin Hajiya Gambo Sawaba da ke Kofar Gayan a Zariya Jihar Kaduna, Dokta Habila Shehu Mu’azu ya musanta zargin sace nau’rar gwaje-gajen marasa lafiya, mai gani har hanji (Endoscopy Machine), mallakar asibitin. Na’urar, wacce Gwamnatin Jihar Kaduna ta sayo a kan miliyoyin Naira domin gwaje-gwajen cututtuka iri-iri, wadansu ne suka tsegunta wa Aminiya bacewarta, ganin yadda al’umma ke amfana da ita.

A can baya, Gwamnatin Jihar Kaduna, lokacin tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Alhaji Namadi Sambo na  Gwamna ne ya sayo na’urorin gwaje-gwajen guda uku.

Gwamnatin ta sayo na’urori ne domin saukaka wa talakawa biyan kudi masu dimbin yawa a asibitoci masu zaman kansu. A wancan lokaci, an raba na’ura  dai-daya  ga kowane yankin Sanata, inda aka kai daya Kaduna,  aka ajiye ta a Asibitin Yusuf Dantsoho, aka kai daya Babban Asibitin Kafanchan; sannan aka kawo daya Asibitin Gambo Sawaba.

Dokta Habila ya ce wurin da aka ajiye ta Zariya, wato dakin da aka sa na’ura bai samu fandisho mai kyau ba, saboda jim kadan bayan sa na’urar sai aka gano cewa ginin na nutsewa kasa, wanda ya tilasta aka tattara ta aka ajiye a wurin ajiyar kayayyaki, domin kada a yi asararta.

Aminiya ta lura cewa barin dakin gwaje-gwajen ba komai kuma babu kowa ciki ne ya sa macizai suka gaje wurin, ya zamo wurin zamansu.

ADVERTISEMENT

Wakilinmu ya fahimci cewa hatta ma’aikatan asibitin suna dari-darin shiga wurin, sai dai shi wakilin namu ya yi ta maza ya leka dakunan amma babu komai ciki sai kura da zanen alamar tafiyar maciji, wanda ke nuna alamun hanyoyin da macizai ke bi suna watayawarsu a cikin ginin.

Da yake yi wa Aminiya karin bayani, Dokta Habila Mu’azu ya ce sun kwashe na’urorin ne sun adana su a sito saboda nutsewa da dakin ke yi. Sannan ya musanta zargin da ake yi cewa na’urar gwaje-gwaje ta bata. Ya ce sanadiyyar lalacewar wani bangare na na’urar da ke Asibitin Dantsoho da ke Kaduna kuma ganin cewa ba a amfani da ta Zariya sai Shugaban Asibitin Kaduna na wancan lokaci, Dokta Hassan Yahaya ya roki a ba su aron wannan bangare na na’urar (Gastroscope Machine), wadda a yanzu haka take Asibitin Barau Dikko, suna amfani da ita kafin a gyara nasu.

Da Aminiya ta tuntubi Dokta Hassan Yahaya na Asibitin Barau Dikko ta waya kan batun daukar aron na’urar, sai ya ce tabbas su ne suka ara amma ta hannun Sakataren Ma’aikatan Lafiya ta Jihar Kaduna, domin wadda suke aiki da ita a asibitinsu ta lalace. Sai dai ya ce yanzu haka ma suna shirin maida musu da ita.

Babban likitan ya ce a yanzu haka an rubuta musu wasika domin su dawo da ita.

Dokta Habila Mu’azu ya roki Gwamnatin Jihar ta duba yiwuwar gina sabon dakin gwaje-gwaje mai inganci,  maimakon yi wa wannan da ake da shi kwaskwarima.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya