Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Madigo: Me ke jefa matan aure a wannan masifa?

Madigo daya ne daga cikin kalmomi mafiya muni a wajen furtawa bayan kalmar luwadi, haka wannan aiki na daga cikin kaba’irori mafiya girma a wajen Allah (SWT). Kafin fara wannan bayani zan so mutane su san cewa, “Allah ba Ya jin kunyar abin da yake gaskiya.” Don haka idan ma kalmomina sun yi tsauri a gafarce ni ita gaskiya sai da rufe ido.

Babban abin da ya fi kawo damuwa da takaici shi ne tsundumar matan aure a cikin wannan kazantacciyar harka da za ta kai duk wadda ta mutu tana aikatawa ba ta tuba ba zuwa ga wuta.

ADVERTISEMENT

To tambayar da ta dame mu shin me ke haifar da madigo a tsakanin matan aure? Wadansu manazarta na ganin sha’awa ce ke sanya wadansu aikata wannan  muguwar dabi’a. Babu shakka akwai sha’awa akwai kuma talauci haka akwai rashin kula da mata da wadansu maza ke yi.

Bari mu fara tsokaci game da sha’awa tukun (domin ita ce mataki na farko). Yawanci matan aure sun raja’a a kan shan kayan karin ni’i’ma ko kayan da’a.

ADVERTISEMENT

To su wadannan kaya, likitoci sun tabbatar da cewa, sukan motso sha’awar mace da kashi 70 ko 80 ciki 100, babu wani abu da take so sama da saduwa. To duk lokacin da ta nemi saduwar a wajen mai gidanta, idan ba ta samu ba, sai ta ji tana sha’awar mace ’yar uwarta. To daga nan sai ta bukaci yin wannan mu’amala ta kazanta. Idan ba a yi sa’a ba shi ke nan sai Shaidan ya yi galaba a kansu.

Rashin samun kula daga mai gida, yawanci magidanta ’yan siyasa da ’yan kasuwa ba su cika bai wa matansu hakkinsu ba, ta yadda idan sha’awarsu ta motsa ba sa samun kula yadda ta kamata.

Wadansu daga cikin wadannan mazan ko sun kula matansu, to ba su biya musu bukata yadda ta dace. Domin idan dan siyasa ne to tunaninsa zai raja’a ak an kamfe ko tarukan siyasa. Idan dan kasuwa ne tunaninsa na wajen kasuwancinsa kuma masana sha’awa sun bayyana tunani a matsayin babban sinadirin da ke sanya rauni ga sha’awar namiji ko mace.

Haka talauci yana daga cikin manyan abubuwan da ke sanya matan aure madigo. Domin yanzu akwai hajiyoyin mata wadanda ba sa samun kula daga mazansu da suka yi nisa cikin wannan muguwar dabi’a ta madigo, a kullum burinsu neman matan aure domin su rika debe sha’awarsu.

Idan irin wadannan mata suka hadu da wacce mijinta bai da karfi kuma suna sha’awarta kai-tsaye za su nuna mata kudi su janye hankalinta. Kuma sukan rudi wadannan mata cewa, madigo yana sanya arziki.

Na taba samun labarin mutumin da matarsa ta bata masa yarinyarsa da wannan abu. Shi wannan mutum ya auro amarya bai san tana harkar ba, yana da yara sai babbar ’yarsa take zuwa taya amaryar kwana in ba girkinta ba ne. An zaci, shakuwa ce mai karfi a tsakaninsu, ashe abin da take koya wa yarinyar ke nan sai da abin ya shiga yarinyar ita ma ta kware an kai ta makarantar kwana aka kama ta tana yi, a nan ta ce matar babanta ce ta koya mata.

Babu shakka duk mai yin wannan dabi’a ta madigo ta san cewa, idan ta mutu ba ta tuba ba, za a kona a wuta. Domin matar Annabi Ludu (AS) duk da matar Annabi ce, lokacin da Allah Ya yi wa Annabi Ludu umarnin  ya bar garin da yake ciki, cewa  Ya yi amma ba ita matar domin ta kasance daga cikinsu.

Sannan masu yin wannan muguwar dabi’a ta madigo su sani yana daga cikin abin da ke haifar da kamuwa da cututtuka. Saboda akwai wata kankanuwar kwayar cuta (parasitic organism) idan wadda ake madigo da ita na dauke da ita, to nan take za ta shafa wa ’yar uwarta cutar.

Haka tana haifar wa masu yin wannan dabi’ar mugun ciwon mara domin duk yadda suka kai ga dabara da kwarewa ba za su taba inzali kamar suna tare da namiji ba.

Don haka ya ke ’yar uwa! Idan ba ki tuba kika bari don Allah ba, ya kamata ki san irin cututtukan da ke jiranki!

Jamilu Sani Rarah, ya rubuti wannan mukala ce daga  Sakkwato kuma za a iya samunsa ta tarho mai lamba: 07031960698