✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Madrid ta janye daga cinikin Gareth Bale

A ranar Talatar da ta wuce ne kocin kulob din Real Madrid da ke Sifen Carlo Ancelotti ya fadawa shugaban kulob din Florentina Perez cewa…

Gareth BaleA ranar Talatar da ta wuce ne kocin kulob din Real Madrid da ke Sifen Carlo Ancelotti ya fadawa shugaban kulob din Florentina Perez cewa ya hakura da yunkurin da yake yi na cefano dan kwallon Tottenham da ke Ingila, Gareth Bale a kakar wasa ta bana.
Kocin ya shaida wa shugaban ne a lokacin da suka yi ganawa ta musamman jim kadan bayan kulob din ya gama wasannin sada zumunta a Amurka kafin ya koma Sifen don tunkakar kakar wasa ta bana da za a fara a gobe Asabar.
  Don haka hasashen da wasu ke yi na ganin kulob din ya nace akan sayo Gareth Bale yanzu ta zo karshe.
Rahotanni sun ce akwai yiwuwar kulob din Manchester United ya shiga batun cinikin Bale tun da Madrid ta hakura a kan cinikin dan kwallon.
 Sai dai masu hasashe na ganin da wuya dan kwallon ya koma United saboda ba shi da sha’awar cigaba da yin kwallo a Ingila.
Tun da farko shugaban kulob din Madrid ya yi yunkurin cefano Bale ne don karfafa ‘yan wasan kulob dinsa musamman  ganin yadda kulob din FC Barcelona ta sayo shahararren dan kwallo Neymar don tunkakar wasa ta bana amma ganin yadda kulob dinsa ya lashe wasanni shida daga cikin bakwai da ya yi a wasannin sada zumunta da aka kammala a karshen makon jiya ta sa shugaban ya canza shawara a kan Bale.
Sannan da yawa daga magoya bayan kulob din Madrid sun nuna shakku a kan tsadar Bale, inda wasu suka nuna bai dace  dan kwallon ya yi tsadar da ta wuce  Fam miliyan 60 a maimakon fiye da Fam miliyan 100 da kulob din ya taya shi ba.  
Haka kuma da yawa daga cikin ’yan kwallon kulob din ba su goyi bayan sayo Bale ba musamman ganin yadda cinikinsa yake neman raba musu hankali a daidai lokacin da suke shirin fuskantar kakar wasa ta bana.