Da Dumi Dumi

Madrid ta yi musayar gola da PSG

A ranar Litinin da ta wuce ana gab da rufe kasuwar cinikin ’yan kwallo, kulob din Real Madrid da ke Sifen ya kulla yarjejeniya da kulob din Paris Saint Germain (PSG) da ke Faransa inda suka yi musayar gololi.

A yayin da golan PSG Alphonse Areola ya koma Madrid shi kuma golan Madrid Keylor Nabas ya canja sheka ne zuwa kuilob din PSG.

Real Madrid ta dade tana zawarcin dan kwallon PSG Neymar Jnr inda suka rika rububi a tsakaninsu da kulob din FC Barcelona amma dukkansu ba su samu nasarar saye dan kwallon ba har aka rufe kasuwar ’yan kwallo a ranar Litinin da ta wuce.  Hakan ya sa Madrid ta karkata akalarta zuwa golan PSG.

Rahotanni sun ce an yi musayar gololin ne a matsayin aro na kaka daya.

ADVERTISEMENT
Share