Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Madrid tana nadamar sayar da Ronaldo

A shekaranjiya Laraba ce rahotanni suka nuna yadda Shugaban Kulob din Real Madrid da ke Sifen Florentino Perez ya ce kulob din ya fara nadamar sayar da dan kwallonsa Cristiano Ronaldo ga kulob din Jubentus na Italiya.

Madrid dai ta sayar da Ronaldo ne ga kulob din Jubentus  na Italiya a kan Fam miliyan 105 (kwatankwacin Naira biliyan 49 da miliyan 455) a farkon kakar wasa ta bara wanda hakan ya jefa kulob din cikin matsala.

ADVERTISEMENT

Lokacin da Mista Perez yake hira da manema labarai ya ce a gaskiya yanzu sun gane kuskurensu na sayar da Ronaldo ganin yadda kulob din yake fuskantar matsala a kakar wasa ta bana.

A halin yanzu kulob din Madrid ne na biyar a jerin kungiyoyin da ke fafatawa a gasar La-Liga ta Sifen inda kulob din FC Barcelona da ke saman tebur a gasar ya ba Madrid tazarar maki goma tun ba a je ko’ina ba.

ADVERTISEMENT

Masoya kungiyar kwallon kafa ta Madrid sun nuna damuwa da mamaki kan yadda kulob din ya sayar da Ronaldo tun kafin ya samu wanda zai maye gurbinsa.