Search
Subscribe
Mafarauta sun kama mesa mai tsawon mita biyar a Jigawa

Mafarautan riqe da mesar

Mafarauta sun kama mesa mai tsawon mita biyar a Jigawa

Wadansu mafarauta a Jihar Jigawa da suka je farautar guza ko tunku a dajin Baranda da ke Karamar Hukumar Dutse, sun samu nasarar kama mesa da ta kai tsawon mita biyar.

Daya daga cikin wadanda suka kama mesar, Malam Abdu Maikano Madobi ya ce sun je dajin ne daga kauyensu mai nisan kilomita 20, inda bayan sun shiga dajin, sai suka ga ramin a zatonsu guza ne a ciki ko tunku saboda haka ne suka dauki magirbai suka hau tonon ramin, inda suka ajiye karnukansu a gefe don shirin ko-ta-kwana.

Maikano ya ce “Da hakarmu ta yi nisa sai na hangi abu bakikirin a cikin ramin. Da muka ci gaba da hakar ramin sai ta yi can ciki. Sai muka ci gaba da haka har muka cim mata. Da muka cim mata sai na ga mesa ce, da yake na je wajen da bindigar toka sai na dauko ta na shiga cikin ramin na kafa ta na daidaici wuyan mesar ta baya na harbe ta. Ganin haka ya sa ta sake yin can ciki na sake fita daga ramin muka yi amfani da wasu manyan hogen kasa muka rufe ramin, na sake kwantawa na sake wa bindigata duri na sake harbinta a baya, na karya mata kashin baya. Shi ne ta yiwo waje sai muka sa gatari muka buge ta a kai, muka kayar da ita muka danne ta muka yanka.”

Ya ce, “Sakamakon haka ne muka bar ta a yanke muka ci gaba da farauta kafin mu fede ta, inda muka bar ta na awa daya tana motsi ganin ta daina motsi shi ne muka fede ta. Kuma mun samu nama da ya kai cikin fanteka babba. Kai hatta fatar mesar nan Naira dubu shida muka sayar da ita.”

Da yake magana game da girman mesar, ya ce girmanta ya wuce duk inda dan Adam yake tunani, domin a cewarsa, tsawonta ya wuce mita biyar, “Ni dai tun da nake kama maciji tun ma muna zuwa da mahaifina ban taba ganin maciji mai tsawon wannan ba,” inji shi.

Ya kara da cewa yanzu haka a dajin sun ga wasu manyan ramuka da suka yi kama da wancan, kuma suna zaton ramin mesan ne kuma shi ne za su koma su ga mene ne a ciki don gane wa idonsu.

Ya ce saboda yawan cin naman maciji, in maciji ya gan shi gudu yake yi, “Amma akwai wasu macizan da sai an ja daga an yi artabu da su suke guduwa saboda wasu macizan suna da matsala,” inji shi.

Ya ce ba shi daya ya kama mesar ba, akwai shugabansa Malam Jibrin Danyau da Alhassan Ubale da kuma Auwalu Wanyo.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin