Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Mafi qarancin albashi: Ba za mu iya biyan Naira dubu 30 ba – Gwamnoni

  • Za mu shiga yajin aikin sai baba ta gani – ’Yan  qwadago

A ranar Litinin da ta gabata ce Qungiyar Gwamnonin Najeriya ta qara nanata matsayarta ta cewa gwamnoni ba za su iya biyan Naira dubu 30 a matsayin mafi qarancin albashi ba.

Gwamnonin sun ce ko ma sun fara, tsarin ba mai xorewa ba ne, kuma yanayin da ake ciki ba yanayi ne da ya dace a yi qarin ba. Maimakon haka, qungiyar ta amince cewa jihohi za su iya biyan Naira dubu 22 da 500 a matsayin mafi qarancin albashin.

ADVERTISEMENT

Sai dai kuma sun ce duk jihar da ta ga ita za ta iya yin qari don kanta, to za ta iya qarawa a kan Naira 22 da 500 xin da suka amince. Gwamnonin sun ce ba gaskiya ba ne cewa da Qungiyar Qwadago  ta Qasa (NLC) ta yi cewa ba su son su biya qarin albashin.

Sun ce suna son biya, amma halin biya ne a yanzu ba su da shi, idan suka yi la’akari da kason da suke karba na kuxi duk wata daga Asusun Tarayya. Kakakin Qungiyar Gwamnonin, Abdulrazak Bello Barkindo ne ya bayyana haka, a cikin wata takarda da ya aike wa manema labarai.

ADVERTISEMENT

A xaya bangaren kuma, Qungiyar NLC ta yi kira ga xaukacin ma’aikatan qasar nan  su fara shirin shiga yajin aikin sai baba ta gani.

Shugaban Qungiyar NLC, Mista Ayuba Wabba ne ya yi wannan kira a shekaranjiya Laraba, inda ya buqaci  Gwamnatin Tarayya ta gaggauta miqa dokar qarin albashin na Naira dubu 30 ga Majalisar Dokoki ta Qasa domin ya zama doka.

Mista Wabba ya ce shekarar 2018 ta zama shekara mafi matsi ga ma’aikatan qasar nan saboda qin amincewa da dokar qarin albashin na Naira dubu 30. Ya ce qungiyar qwadago da ma’aikatan  qasar nan, sun gaji da kwan-gaba-kwan-bayan da gwamnati ke yi wajen qin cika alqawarinta na qarin albashin.

“Don haka muna umartar ma’aikata a faxin Najeriya su shiga shirin fara yajin aiki wanda ba a san ranar dawowarsa ba. Domin hakan zai tilasta wa gwamnati amincewa da qarin albashin na Naira dubu 30.