Da Dumi Dumi

Magajin Garin Daura ya gana da iyalansa

Masu garkuwa da mutane sun tuntubi iyalan Magajin Garin Daura Alhaji Musa Umar  Uba awanni bayan sun yi garkusa da shi.

Wakilinmu ya tabbatar da cewa basaraken, wanda suruki yake wajen Buhari, kuma surukin dogarin  Buhari ya gana da iyalansa kuma yana cikin koshin lafiya.

Idan ba a manta ba, mun ruwaito yadda masu garkuwa da mutane suka yi shigan burtu suka sace basaraken a kofar gidansa jim kadan bayan sallar Maghariba.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya