✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Magajin Garin Daura ya samu gagarumar tarba

Magajin Garin Daura, Alhaji Musa Umar Uba, ya samu gagarumar tarba bayan da ya koma gida Daura shekaranjiya Laraba. Hakan ya biyo bayan kwato shi…

Magajin Garin Daura, Alhaji Musa Umar Uba, ya samu gagarumar tarba bayan da ya koma gida Daura shekaranjiya Laraba.

Hakan ya biyo bayan kwato shi da aka yi daga hannun wadanda suka yi garkuwa da shi a ranar 3 ga watan Yuli, inda ya shafe wata biyu a hannunsu. An dai yi garkuwa da Magajin Garin Dauran ne a ranar 1 ga watan Mayu, a garin Daura, inda aka kwato shi ne a Kano bayan wata biyu.

Da isarsa garin Daura, sai ya ya zarce zuwa Fadan Mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk wanda wansa ne, inda ya samu tarba daga hakimai da sauran masu sarautun gargajiya na masarautar.

Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk, ya bayyana garkuwa da Magajin Garin Dauran, a matsayin mummunan al’amari: “A madadina da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da daukacin al’ummar Masarautar Daura muna godiya ga Allah da Ya dawo mana da Magajin Garin Daura da ransa. Muna kuma godiya ga dukkan ’yan Najeriya da wadansu a Jamhuriyar Nijar da Ghana; wadanda suka yi ta aike mana da sakonnin karfafa gwiwar da rokon Allah Madaukakin Sarki Ya kwato Magajin Garin Daura,” inji Sarkin.

Mutane sun yi cincirindo suna murna da dawowar Magajin Garin, sai dai Magajin Garin, bai gana da manema labarai ba.