✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Magidanci ya shiga layin zabe shekaranjiya Laraba a Jos don fara zabar Buhari

Wani magidanci mai suna Abubakar Shettima da ke Unguwar Duala da ke Dogon Dutse a Karamar Hukumar Jos ta Arewa ya kwashi nasa-ya-nasa ya kafa…

Wani magidanci mai suna Abubakar Shettima da ke Unguwar Duala da ke Dogon Dutse a Karamar Hukumar Jos ta Arewa ya kwashi nasa-ya-nasa ya kafa layin zabe a rumfar da yake kada kuri’a a shekaranjiya Laraba domin sake kada wa Shugaba Buhari kuri’a.

Abubakar mai shekara 59, ya ce ya yi sammakon zuwa layin zaben ne domin yana so ya kasance mutum na farko da ya kada wa Shugaba Buhari kuri’a a zaben gobe, wanda a cewarsa yake so ya zama tukuici ga Shugaban Kasar bisa taimakonsa da ya yi wajen kwato masa ’yanci bayan an zarge shi da kasancewa dan Boko Haram a shekarar 2015.

“Yanzu haka na tura matata Jihar Borno da safiyar yau (jiya Alhamis) domin ta kada kuri’a, sannan ina da ’ya’ya uku wadanda dukansu sun isa yin zabe. Biyu daga cikinsu za su zabi Buhari gobe Asabar a nan Jos, daya kuma ta yi aure tana Maiduguri, wannan kuma sai yadda mijinta ya so,” inji shi.

Wakiliyarmu ta  iske Malam Abubakar zaune a kan darduma rike da Kur’ani a wata rumfa da aka lika sunayen masu kada kuri’a na wannan akwati, kuma katin zabensa na dindindin yana aljihunsa.

Abubakar dan asalin Jihar Borno ne, ya ce shi da wadansu daruruwan mutane an taba kama su ba gaira, ba dalili wai ana zargin cewa su ’yan Boko Haram ne a shekarar 2015.

“A Tashar Motar Bauchi na Jos aka kama ni tare da wadansu mutane aka kai mu Jihar Bauchi, daga can aka kai mu Yobe, sannan aka mayar da mu Borno inda aka kulle mu na watanni. Amma bayan Shugaba Buhari ya lashe zabe, sai ya ziyarci inda aka kulle mu, da ya ga halin da muke ciki, sai ya bayar da umarnin cewa a rage yadda muke a cakude, a sanya mutum 200 a kowane daki kafin a kammala bincike.”

Malam Abubakar ya ce bayan an kammala binciken, sai aka gane cewa ba su da laifin komai, Ya ce “Kafin a sake mu sai da Gwamnan Jihar Borno Kashim Shettima ya ba mu hakuri, sannan ya ba mu Naira dubu goma-goma domin mu koma gida. Don haka domin tukuici ga Shugaba Buhari wanda ba don shi ba, da watakila ba a sake mu ba, nake addu’ar Allah Ya sa ya ci gaba da mulki saboda talakawa suna tare da shi.”