Da Dumi Dumi

Magidanci ya watsa wa mutum 30 guba a Kuros Riba

Ana zargin wani magidanci mai suna Ogar Ogbudu da ke yankin Ugaga a Karamar Hukumar Yala a Jihar Kuros Ribas da watsa wa sama da mutum 30 sama da ruwan batir (guba) kan zargin zaluntar dansa da abokan dan suka yi lokacin da suke wasa a  dandalin unguwa.

Wani mazaunin kauyen Ugaga mai suna Omgbidu Sabour, ya shaida wa Aminiya cewa, “Fada ne irin na yara ya barke a tsakanin tsararrakin dan Ogbudu, shi kuma yaron sai ya ruga gida ya sanar da mahaifinsa abin da abokansa suka yi masa, shi ne ya fusata ya yi wannan aika-aika.”

Ya ce, yaran shekarunsu suka kama daga 14 zuwa 15, sun taru dandalin unguwa suna wasanninsu  ne kamar yadda suka saba.

“Sai yaron ya ruga gida ya dawo da shirin fada ganin haka ne sai wadansu daga cikin manyan gari suka je suna sasanta su, shi kuma Ogar Ogbudu, da ya zo bai yi wata-wata ba ya watsa wa mutanen da ke sulhun ruwan guba,” inji Sabour.

Mutanen da aka watsa wa ruwan gubar sun kai mutum 30. An kwashe wadanda gubar ta shafa zuwa asibitin Igoli da ke Karamar Hukumar Ogoja, domin yi musu magani. Da wakilinmu ya tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kuros Riba, DSP Irene Ugbo ta tabbatar da faruwar hakan, inda ta ce sun fara bincike a kan lamarin.

ADVERTISEMENT
Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya