✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Magoya baya sun lakada wa shugaban wani kulob duka a Ajantina

Magoya bayan wani kulob mai suna Club Atletico Independiente da ke buga gasar rukuni-rukuni ta Ajantina sun lakada wa shugaban kulob din Jabier Cantero dukan…

Magoya bayan wani kulob mai suna Club Atletico Independiente da ke buga gasar rukuni-rukuni ta Ajantina sun lakada wa shugaban kulob din Jabier Cantero dukan kawo wuka bayan da kulob din ya samu koma baya a karshen gasar rukuni-rukuni ta kasar a karshen makon jiya.
Al’amarin ya faru ne a lokacin da shugaban yake jawabi ga magoya bayan kulob din a hedkwatar kulob din da ke Abellaneda da ke yankin Kudancin Buenos Aires.
Jifar da suka rika yi wa shugaban da kujeru da kwalabe da kuma duwatsu ta sa ala tilas ya ranta a- na-kare don tsira da rayuwarsa.
Su dai magoya bayan sun zargi shugaban kulob din ne da laifin rashin iya gudanar da mulki da hakan ta sa kulob din ya samu koma-baya zuwa matakin ’yan dagaji&nbsp