✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Magoya bayan Marseille sun yi wa Neymar a ture

A ranar Lahadin da ta wuce ne magoya bayan kulob din Marseille da ke buga gasar rukuni-rukuni na Faransa suka rika jifar dan kwallon PSG…

A ranar Lahadin da ta wuce ne magoya bayan kulob din Marseille da ke buga gasar rukuni-rukuni na Faransa suka rika jifar dan kwallon PSG Neymar da fasassun kwalabe da robar ruwa da kuma duwatsu kamar yadda kafar watsa labarai ta The Sun da ke Ingila ta ruwaito.

A wasan PSG ce ta bi Marseille har gida ta lallasata da ci biyu babu ko daya da hakan ya sa kulob din ya lashe wasanni 11 kuma kawo yanzu ya ba da tazarar maki takwas a matsayin kulob din da ke jagorantar gasar.

Haka kuma magoya bayan Marseille sun jefi Kylian Mbappe da Julian Dradler don nuna bacin ransu a wasan.

Wannan ba shi ne karo na farko da magoya bayan Marseille suka taba jifar Neymar da duwatsu ba.  A watan Obtoban bara ma, magoya bayan sun jefi Neymar jim kadan bayan alkalin wasa ya ba shi jan kati a wata keta da ya yi.