Daily Trust Aminiya - Magoya bayan PDP da PDM dubu 10 sun sauya sheka zuwa APC a J
Subscribe

Magoya bayan PDP da PDM dubu 10 sun sauya sheka zuwa APC a Jihar Kebbi

Sama da magoya bayan Jam’iyyar PDP da PDM dubu 10 suka sauya sheka zuwa Jam’iyyar APC a Jihar Kebbi a makon jiya.
Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDM a shiyyar Kebbi ta Kudu Alhaji Mohammed Sani Zuru ne ya jagoranci shugabannin jam’iyyar na kananan hukumomin jihar 21 da magoya bayansu zuwa APC.
A wani gaggarumin taro da aka yi a ofishin Jam’iyyar APC, jiga-jigan PDP da suka rufa masa baya sun hada da wani na hannun daman Gwamnan Jihar Kebbi Alhaji Sani Dodo da tsohon shugaban Jam’iyyar PDP na jihar Alhaji Sani Hukuma Zauro, Zannan Gwandu da magoya bayansu daga kananan hukumomin jihar.
Da yake jawabi a wurin karbarsu, shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kebbi Alhaji Atiku Bunu Jega ya ce ya rasa abin da zai ce saboda murna domin gaskiya ta yi halinta.
Shugaban ya ce su da suka dade a cikin APC da wadanda suka shigo ta a ranar sun zama daya, kuma da yardar Allah za a yi masu adalci.
Alhaji Bunu Jega ya shaida masu cewa Jam’iyyar APC ba jam’iyyar masu nadi ba ne jam’iyya ce mai bin ka’idoji da doka da oda kowane mukami za a zabe shi ne kamar yadda tsarin mulkinta ya tanada.
A jawabin Alhaji Sani Dodo ya ce a halin yanzu duk inda aka shiga a kananan hukumomin jihar, za a tarar da dubban mutane a kullum suna ta fita daga PDP zuwa APC. Ya ce rashin adalcin Gwamnan Jihar inda ya maida mutane ba bakin komai ba, ya sa jihar ta koma kamar makabarta babu mai motsi ko me cewa wani abu.
Ya yi kira ga al’ummar jihar su kara hakuri zuwa nan da zaben badi, inda za su ga canji a kan irin matsalolin da suke damunsu muddin Jam’iyyar APC ta kafa Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Kebbi.

texem
More Stories