✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Magoya bayan Real Madrid sun yi zanga-zanga

A ranar Talatar da ta wuce magoya bayan kulon din Real Madrid da ke Sifen da dama suka gudanar da wata zanga-zanga don nuna fushinsu game…

A ranar Talatar da ta wuce magoya bayan kulon din Real Madrid da ke Sifen da dama suka gudanar da wata zanga-zanga don nuna fushinsu game da yadda kulob din Ajad da ke Holland ya lallasa na Madrid da ci 4-1  a gida wanda hakan ya sa kulob din ya yi ban-kwana daga gasar Zakarun Kulob na Turai.

A wasan farko Madrid ce ta bi Ajad har gida ta lallasa ta da ci 2-1 amma abin mamaki sai Ajad ta bi Madrid har Sifen ta yi mata luguden kwallaye 4-1.

Jim kadan da kammala wasan ne sai magoya bayan kulob din suka fantsama a kan tituna suna yi wa Shugaban Kulob din Florentina Perez tofin Allah-tsine da kuma neman a kori kocin riko Santiago Solari ba tare da bata lokaci ba.  Haka kuma masu zanga-zangar sun nemi  kulob din ya sake  ba Jose Mourinho dama don ya sake zama kocin kulob din  a karo na biyu.

Kulob din Manchester United ne ya kori Jose Mourinho a watan Disamban bara saboda rashin kokari, amma sai ga shi magoya bayan Madrid suna neman a dauko musu shi don ya maye gurbin kocinsu na yanzu Solari.

Tun bayan da kulob din Real Madrid ya rabu da dan kwallonsa Cristiano Ronaldo da tsohon Koci Zinedine Zidane ya shiga matsala don alamu sun nuna a kakar wasa ta bana kulob din ba zai lashe wani kofi ba.