✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahaifi ya makure ’yarsa mai shekara 4 ya binne gawarta a dakinsa

“Yan sanda a Jihar Jigawa sun kama wani matashi mai suna Nasiru Hamisu da ke garin Gujungu a Karamar Hukumar Taura bisa zarginsa da laifin…

“Yan sanda a Jihar Jigawa sun kama wani matashi mai suna Nasiru Hamisu da ke garin Gujungu a Karamar Hukumar Taura bisa zarginsa da laifin makure ’yarsa ’yar shekara hudu a duniya mai suna Zainab Hamisu har ta mutu. Kuma ana zargin bayan ta rasu ne sai Hamisu ya haka rami a cikin dakinsa da yake kwana ya binne ta.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa SP Audu Jinjiri wanda ya rabbatar da faruwar lamarin, ya ce lokacin da Hamisu ya amshi yarinyar daga wajen mahaifiyarta kowa ya yi zaton kwantar da ita zai yi saboda tana barci, saboda haka da ya dauke ta babu wanda ya hana shi.

Kuma babu wanda ya san abin da Hamisu ya aikata a kan ’yarsa Zainab sai da gari ya waye ana ta cigiyar Zainab ba a ganta ba sannan aka je dakin mahaifin nata sai aka ga tudu shi ne aka bude sai aka ga gawar Zainab a binne ta.

Kakakin ’Yan sandan ya shaida wa manema labarai cewa dama can Nasiru ya sha yin tsirara yana kewaya garinsu na Gujungu ya kara da cewa mutum da ake zargi da mu’amala da kwayoyi kuma ana zarginsa da tabin hankali

Ya ce duk da hakan wanda ake zargin yana hannun jami’an tsaro na farin kaya ana gudanar da bincike a kan al amarin kuma da zarar ’yan sanda sun kammala bincike za su gurfanar da Nasiru a gaban kotu domin a yi masa hukuncin da ya dace.