✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahaifin Babban Editan Daily Trust ya rasu

Mahaifin Babban Darakta/Babban Edita a kamfanin Media Trust Limited (Mai wallafa jaridun Daily Trust da Aminiya), Malam Miko Alhassan ya rasu. Malam Alhassan ya rasu…

Mahaifin Babban Darakta/Babban Edita a kamfanin Media Trust Limited (Mai wallafa jaridun Daily Trust da Aminiya), Malam Miko Alhassan ya rasu.

Malam Alhassan ya rasu a ranar Litinin a Kano bayan ya yi fama da gajeriyar rashin lafiya.

An haifi marigayin mai shekaru 89 a garin Gora da ke karamar hukumar Madobi a jihar Kano.

Gabanin rasuwarsa, Malam Alhassan yana zaune ne a rukunin gidaje da ke unguwar Koki a birnin Kano.

Ya rasu yana da mata daya da ‘ya ‘ya 16 wanda biyu daga cikinsu suka hada da Babban Darakta/Babban Edita a kamfanin Media Trust Limited (Mai wallafa jaridun Daily Trust da Aminiya), Naziru Mika’ilu da Maikano Miko, mukaddashin shugaban tsangayar ilimin manya kuma tsohon shugaban sashen koyar da kimiyya ta (Physics) a Kwalejin Ilimi na Sa’adatu Rimi da ke Kano.

An yi jana’izarsa bisa tsarin addinin Musulunci ranar Litinin a makabartar da ke Kofar Mazugal a Kano.

A sakon ta’aziyyarsa, Shugaban kamfanin na Media Trust, Malam Mannir Dan-Ali, ya ce marigayin ya samu wadatacciyar rayuwa kuma za a yi rashin hikimomi da shawarwarinsa.

“Allah Ya shigar dashi aljannar firdausi kuma ya bai wa iyalansa hakurin rashinsa,” in ji shi.