Daily Trust Aminiya - Mahaifin Bill Gates ya mutu yana da shekaru 94
Subscribe

Bill Gates da mahaifinsa, William Henry.

Mahaifin Bill Gates ya mutu yana da shekaru 94

William Henry Gates II, mahaifin hamshakin attajirin nan da ya kirkiri kamfanin Microsoft, Bill Gates, ya rasu ranar Litinin yana da shekaru 94 a duniya.

Iyalan Henry sun shaida wa jaridar New York Times cewa cutar Alzheimer’s ce ta yi sanadin mutuwarsa.

Marigayi William tsohon soja ne kuma yana cikin manyan lauyoyin da suka kirkiri wani kamfani da ake kira Seattle Law Firm.

“Za mu yi kewar shi fiye da yadda ake tsammani. Muna cikin matukar bakin ciki da godiya ga Allah,” inji dansa Bill Gates mai shekara 64 a yayin da ya ke bayyana mutuwarsa a kafar sadarwarsa ranar Talata.

“Hikimarsa da karamcinsa da fahimtar mutane da kuma rashin girman kai sun taimaka wa mutane a duniya baki daya.”

Bill Gates ya bayyana alhininsa musamman saboda yadda mahaifin nasa ya taimaka wa rayuwarsa da ta kanwarsa inda ya ce sun yi ‘matukar sa’a’ da Allah Ya ba su iyayen da ke ba su kwarin gwiwa tare da hakuri da su.

Ya kuma ce mahaifin nasa shi ne jigon fara Gidauniyar tallafa wa al’umma ta Bill & Melinda Gates wadda ya kirkira tare da matarsa, Melinda.

“Ba don mahaifina ba, da Gidauniyar Bill & Melinda Gates ba ta kai inda take a yau ba,” inji Bill Gates.

Mahaifin nasa ne ya rika shugabantar Gidauniyar tun da aka kirkire ta cikin shekara ta 2000.

Gidauniyar ce abin da hamshakin attajirin a yanzu ya mayar da hankali a kai bayan ya yi murabus daga shugabancin kamfaninsa na Microsoft.

texem
More Stories