✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahaifin Iheanacho na neman dansa ruwa a jallo

dan kwallon Golden Eaglets Kelechi Iheanacho ya bace sama ko kasa, kamar yadda mahaifinsa mai suna James Iheanacho ya tabbatar wa duniya haka a lokacin…

dan kwallon Golden Eaglets Kelechi Iheanacho ya bace sama ko kasa, kamar yadda mahaifinsa mai suna James Iheanacho ya tabbatar wa duniya haka a lokacin da tashar Hot FM ta Owerri take hira da shi a ranar Juma’ar da ta wuce.
“Ban san inda dana ya shiga ba, yau kimanin kwanaki uku kenan rabon da na ganshi ko na same shi a waya”, inji James.
Sai dai rahotanni su nuna mai yiwuwa dan nasa mai kimanin shekara 17 ya tsallake zuwa kasar Turai ne tare da wani ejen don sanya hannu a wani kulob ba tare da sanin mahaifin ba.
A kwanakin baya dai an ruwaito mahaifin Iheanacho sun samu sabani a kan kulob din da yakamata ya sanya wa hannu a kasashen Turai don cigaba da wasa.  Yayin da Iheanacho ya nemi mahaifinsa ya kyale shi ya bugawa kulob din FC Porto da ke Fotugal, shi kuwa Mista James ya bukaci dan nasa ne ya sanya hannu a kulob din Chelsea ko na Manchester City da ke Ingila.