✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahaifin su mawaki Umar M. Shareef ya rasu

Allah Ya yi wa mahaifin mawaki Umar M. Shareef da jarumi Abdum M. Shareef da Mustafa M. Shareed rasuwa. Umar ne ya wallafa a shafinsa…

Allah Ya yi wa mahaifin mawaki Umar M. Shareef da jarumi Abdum M. Shareef da Mustafa M. Shareed rasuwa.

Umar ne ya wallafa a shafinsa na Instagram cewa, “Innalillahi wa inna ilaihirraji un, ina mai alfahari da samun mahaifi kamarka, domin kuwa ka yi mana dukkan abin da ya kamata mahaifi ya yi wa ’ya’yansa. Allah Ya jikanka da rahama Allah Ya gafarta maka. Allah Ya sanya Aljannan ta zama mazauninka. Allah Ya yafe maka dukkan kurakuranka. Ya ubangiji muna godiya a gareka.

Tuni jarumai da sauran masu ruwa da tsaki a masana’antar Kannywood suke taya jaruman jaje da ta’aziya