✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahaifina ya bar Naira Dubu 7 a matsayinsa na tsohon Shugaban kasa – Dan Murtala

Dan tsohon Shugaban Kasar Najeriya Marigayi Janar Murtala Muhammed, mai suna Risqua Muhammed, ya ce, mahaifinsa ya rasu ya bar Naira dubu 7 kacal a…

Dan tsohon Shugaban Kasar Najeriya Marigayi Janar Murtala Muhammed, mai suna Risqua Muhammed, ya ce, mahaifinsa ya rasu ya bar Naira dubu 7 kacal a asusun ajiya na bankinsa duk da ya rike mukamin shugaban kasar Najeriya.

Risqua, ya bayyana hakan ne a lokacin kaddamar da mutum mutumin mahaifinsa a zauren karatun digiri na biyu a jami’ar Obafemi Awolowo, Ile-ife, jihar Osun. Inda aka sanyawa sabon ginin sunan Murtala Muhammed.

Risqua Muhammad, ya ce a yanzu haka mahaifinsa ya rasu shekara 43 da suka wuce kuma ya shugabanci Najeriya cikin adalci.