✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahaifiyar Galadiman Katagum ta rasu

Allah Ya yi wa mahaifiyar Galadiman Katagum, Hakimin Zaki da ke Jihar Bauchi Alhaji Usman Mahmood, wato Hajiya Khadija Mustapha Abdulkadir wacce aka fi kira…

Allah Ya yi wa mahaifiyar Galadiman Katagum, Hakimin Zaki da ke Jihar Bauchi Alhaji Usman Mahmood, wato Hajiya Khadija Mustapha Abdulkadir wacce aka fi kira da Mama Goggo rasuwa.

Ta rasu ne a shekaranjiya Laraba a Asibitin Kasa da ke Abuja, bayan ta yi fama da jinya.

Mama Goggo ta rasu tana da shekara 90 a duniya, kuma ta rasu ta bar ’ya’ya da jikoki da ’yan uwa da dama.Daga cikin ’ya’yanta akwai Galadiman Katagum, Hakimin Zaki Alhaji Usman Mahmood da Alhaji Atta’ib Mahmouod da Hajiya Saddika Mahmod da Abdul-Rashid Mahmood da Hajiya Baheejjah Mahmood da Abdul-Latif Mahmood da Hasur Mahmood.

Daya daga cikin ’ya’yanta Hajiya Baheejjah Mahmood ta shaida wa Aminiya cewa Mama Goggo duk da halin jinya da take fama da shi sai da ta je aikin Hajjin bana.

Ta ce mahaifiyarsu mace ce mai son Allah da son addini da tsabta da son yin Sallah da yawaita addu’o’i da son zumunci da hada kan jama’a, kuma kowa nata ne, inda ta ce ta rasu ta bar gibi mai wuyar cikewa, “Sai dai mu yi ta mata addu’a Allah Ya gafarta mata,” inji ta.

An yi jana’izar ta bayan Sallar Isha’i a shekaranjiya Laraba a Masallacin Kasa da ke Abuja. Allah Ya yafe mata kura-kuranta, Ya sa Aljanna ce makomarta.

Dan Shehun Borno ya kade jami’in tsaro saboda hana su wasan mota

Rahotanni sun ce daya daga cikin ’ya’yan Shehun Borno, mai suna Kashim Abubakar-Elkanemi ya kade wani jami’in tsaro na farin kaya, Cibil Defence lokacin da suke wasan tseren mota a Maiduguri.

Lamarin ya faru ne a lokacin da jami’in tsaron mai suna Usman Bakari, wanda shi ne babban jami’in hukumar mai kula da cikin garin Maiduguri ya bukaci a bar wasan tseren motocin.

Jaridar Daily Nigerian ta ce, wani ganau ya shaida wa kafar labarai ta PFNigeria cewa lamarin ya faru ne lokacin da “Bakari ya zo ya roke mu a bar tseren motocin, sai wadansu matasa suka fara zaginsa, suna cin mutucinsa. Sai wadansu suka fara cewa shi wane ne da zai hana dan Shehun Borno yin abin da ya ga dama. Suna cewa ai kasar mahaifinsa ce. Ana cikin haka ne wasu motoci biyu suka yi kan Bakari, sai ya kauce da kyar. Amma sai dan Shehun ya juyo da mota  ya yi kansa, inda ya buge shi, sauran kuma suka sake kaucewa,” inji majiyar

PRNigeria ta ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:30 na yamma a Dandalin Ramat da ke Maiduguri a ranar Asabar da ta gabata.

Wani faifan bidiyo da kafar ta ce ta gani ya nuna yadda wata mota kirar Fijo 406 ta banke jami’n ya tashi sama kafin ya fado kasa. Kuma nan take motar ta gudu. Shi kuma jami’in wanda ya samu rauni an kais hi Asibitin Kwararru na Maiduguri don yi masa jinya.

Kuma ta ce jami’an Hukumar NSCDCna Jihar Borno sun kama mutum daya da ake zargi da hannu a lamarin, yayin da dan Shehun Bornon ya tsere.