Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Mahaifiyar jaririyar da aka sace a asibiti ta karbi ‘yarta

Hukumar gudanarwa ta babban asibitin Filato a yau Litinin ta mika jaririyar da aka sace ga iyayen jaririyar na asali don tabbatar da jaririyar na cikin koshin lafiya.

Daraktan nas na asibitin da shugaban asibitin da sauran likitocin asibitin da ‘yan uwa sun halarci wajen da aka mika jaririyar kamar yadda manema labarai suka tabbatar.

ADVERTISEMENT

Iyayen jaririyar da aka sace Nwa God Chukwuebuka da Mary Chukwuebuka sun gode wa jama’ar da suka ba su gudunmawa da taya su addu’ar dawo da ‘yarsu.

ADVERTISEMENT