Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Mahaifiyar marigayi Okwaraji ta nemi gwamnatin tarayya ta karrama danta

samuel okwaraji

Janet, mahaifiyar Samuel Okwaraji, ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta yi wa Allah ta karrama danta Samuel da Allah Ya yi wa rasuwa a lokacin da yake bugawa Najeriya kwallo kimanin shekaru 30 da suka wuce.

Samuel Okwaraji, yana daga cikin ’yan kwallon Najeriya Super Eagles.  Ya rasu ne a ranar 12 ga watan Agustan 1989 a ranar da Najeriya take karawa da kasar Angola a gasar neman zuwa cin kofin duniya da aka yi a filin wasa na kasa da ke Legas.  Ana tsakiyar wasa ne Samuel Okwaraji ya yanke jiki ya fadi, kafin a garzaya da shi asibiti rai ya yi halinsa, inda Likitoci suka ce ya kamu ne da matsalar bugun zuciya (heart attack).

ADVERTISEMENT

Misis Janet, ta yi wannan koke ne a ranar Litinin da ta wuce a gidanta da ke Enugu a ranar Uwa ta Duniya (Mothers Day) ta ce abin takaici ne yadda gwamnatin tarayya ta yi biris da yi musu wani abu, musamman wajen karrama danta Okwaraji da ya rasu a lokacin da yake yi wa kasa hidima.

Ta ce marigayi Sam ba don kudi ya buga wa Najeriya kwallo ba, don a wancan lokaci yana zuwa ne daga Jamus wurin da yake karatun digirinsa na uku, kuma a lokuta da dama da kudin aljihunsa yake amfani a gayyatar da ake yi masa na bugawa kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles, amma abin takaici bayan shekara 30 da rasuwarsa har yanzu gwamnatin tarayya ba ta yi masa ko iyalansa komai ba.

ADVERTISEMENT

Ta ce yanzu ta yanke shawarar gina wata babbar makaranta ce inda za ta sanya sunan Samuel Okwaraji don a ci gaba da tunawa da shi.

Shi ma Yayansa Patrick ya nuna takaicin ganin yadda gwamnatin tarayya ba ta karrama kaninsa Sam ba.  Ya ce yana filin kwallon a ranar da abin ya faru, kuma ba zai taba mantawa da ranar ba.  Sai dai “yadda gwamnati ta yi biris da batun Sam zai sa ’yan kwallo masu tasowa su shiga tunani wajen bautawa kasar nan a fagen kwallon kafa.