Wani tsoho da yake da yawan tsawan rai mai shekaru 130 dan kasar Indonesiya mai suna Hajji Ohi Aydarous Samri, ya kasance wanda aka karrama a masaukin baki na Sarkin Saudiyya wato Sarki Salman kuma zai gudanar aikin Hajjin bana da umra tare da iyalansa.
Masauratar Sarkin Salman ta gayyaci Samri masarautar tare da iyalansa shida don gudanar da aikin hajjin bana da Umra.
Jakadan Saudiyya a kasar Indonesiya Essam Al-Thaqafi, ya ce sun gaisa da Hajji Ohi Aydarous Samri tare da iyalansa lokacin da suke filin kjirgin saman Indonesiya kafin su isa filin jirgin saman Sarki Abdullaziz da ke Jeddah.
Sarkin Salman ako wasce shekara yana gayyata mutane da dama don sauke farali a kasa mai tsarki.