✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahajjatan Yobe sama da dubu 1,200 ne za su sauke farali – Bukar Kimen

Zababben shugaban Hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Yobe Alhaji Bukar Kime, ya bayyana cewa sama da Mahajjata dubu 1,200 ne suke shirin sauke farali…

Zababben shugaban Hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Yobe Alhaji Bukar Kime, ya bayyana cewa sama da Mahajjata dubu 1,200 ne suke shirin sauke farali a wanann shekarar da muke ciki daga jihar.

Alhaji Bukar Kime, ya bayyana hakan ne a lokacin zantawarsa da Aminiya inda ya ce duk shirye-shirye da suka jima suna yi anan Najeriya da kasar Saudiya yanzu sun kammala. Ya ce, a can kasa mai tsarki sun kammala samar da masauki a birnin Madina da abincin da za’a basu da shirye-shiryen barin su Madina zuwa birnin Makka.

Shugaban hukumar, ya kuma ce haka a birnin Makka an kama gida a kusa da Masallacin Bin-Ladeen wanda bai da nisa da Masallacin Harami zai kuma dauki Alhazai fiye da dubu 2, kuma Alhazan su na Yobe za su sauka a wajen. Har ila yau Alhaji Bukar Kime, ya kara da cewa Kamar a birnin Jidda ma an gama kwangilar abincin da za’a bai wa Alhazai, haka zaman Mina da Arfa nan ma basu da wata Marsala sun gama komai.

A bangaren lafiya ya ce akwai likitoci guda takwas da magunguna na kimanin Naira miliyan uku da za su bi Alhazan da su. An kuma kammala shirin jigilar alhazai da za su tashi a jirgi na biyu.

Alhaji Bukar Kime, ya kuma kara da cewa sai dai har yanzu ba’a sa ranar fara tashin Alhazan ba suna jiran kamfanin jiragen da zai dauke su ne na Mid-view ya basu lokaci. Daga nansai yace ba su fuskanci kowanne irin kalubale ba wajen bita da sauran su inda ya hori Alhazan da su zama jakadu na gari su kuma yi wa Najeriya da jihar Yobe addu’o’in na dorewar zaman lafiya dangane da rikice-rikicen da ke faruwa musamman a shiyar Arewa maso Gabas na Najeriya.