Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Mahaka ma’adanai a Osun sun koka da kutsen ‘yan kasar China

Sarkin Hausawan Arah Alhaji Muhammadu Mai Jega Da Alhaji Habibu
Sarkin Hausawan Arah Alhaji Muhammadu Mai Jega Da Alhaji Habibu

Wadansu masu kanana da matsakaitan kamfanonin hakar ma’adinai da ke aiki a garin Ilesha da wasu yankunan da ake aikin hakar ma’adinai a Jihar Osun sun koka da kutsen da suka ce ’yan kasar China suna yi wa sana’arsu da suka gada iyaye da kakanni.

Alhaji Isiyaku Muhammad daya daga cikin masu matsakaitan kamfanonin hakar ma’adinai a garin Ilesha ya shaida wa Aminiya cewa, a halin yanzu masu sana’ar hakar ma’adinai a yankin suna cikin wani yanayi na rashin tabbas saboda irin kutsen da ’yan kasar China suke yi wa sana’ar. Ya ce a baya suna gudanar da harkokinsu cikin kwanciyar hankali ba tare da fargabar barayi ko masu garkuwa da mutane ba, amma tun lokacin da ’yan kasar China suka shiga sana’ar suka lalata suka bai wa batagari dama. “Muna zargin su Turawan kasar China ke haddasa rikici domin su mamaye mana sana’armu, wacce ita muka sani tun iyaye da kakkani. Yau sama da shekara 60 ke nan muke wannan harka cikin kwanciyar hankali da salama amma cikin shekara uku  da ’yan China suka shiga sana’ar sun jawo mana fargaba da tashin hankali. A da mutum zai sayi gona ya shiga daji tare da yaran aikinsa babu wata fargabar komai, amma a yanzu sun kawo mana barayi da masu garkuwa da mutane. Don a kwanaki sai da aka sassari yarana a daji, sannan akwai ma’aikacinmu da aka sace sai da ya yi kwana 6  kafin a samo shi, ba mu iya wata sana’a ba sai wannan, da ita muke kula da iyalinmu mu biya kudin makarantar ’ya’yanmu a matsayinmu na ’yan kasa da muke wannan aiki bisa ka’ida. Muna da takardun izini don haka muna kira ga gwamnati ta kawo mana dauki,” inji shi.

ADVERTISEMENT

Alhaji Habibu, daya daga cikin shugabanin masu hakar ma’adinai a garin Ilesha, ya shaida wa Aminiya cewa suna aikin hakar zinariya da sauran ma’adinai a yankin cikin sahalewar gwamnati tare da al’ummar yankin. Ya ce tsarin da suke bi wajen aikin nasu ba ya barazana ga muhalli da lafiyar al’ummar yankin. “Domin ba ma amfani da wasu sinadari ko kayayyakin haka, ba ma yin haka wankewa muke yi, idan ka gan mu muna aiki za ka dauka masu wankau ne na kayan tufafi domin ba ma yin wata alama ba ma yi wa kasa illa. Muna aikin ne a kan gabar ruwa a sama-sama a nan ne muke wanke tabo muna lalubar ma’adanan a ciki,  ruwan da muke aiki a ciki ba ya sauya launi domin shi muke sha da ibada da wanke jiki, don haka a nan babu matsalar nan ta gubar dalma ba a kuma a taba samun barkewar cututtuka a dalilin aikinmu a wannan yanki ba. Kuma aikinmu ba ya barazana ga muhalli. Amma mutanen China suna sauya fasalin kasa domin suna amfani da manyan injuna, sarakunan gargajiya ne ke daure musu gindin haka za ka ga suna tafe ’yan sanda na yi musu rakiya da manyyan makamai,” inji shi.

Sarkin Hausawan yankin Alhaji Muhammad Mai Jega, ya shaida wa Aminiya cewa tun fari sana’ar goro ce ta zaunar da ’yan Arewa a Jihar Osun. Ya ce lokacin da ta gushe sai suka koma sana’ar katako, “Yanzu haka sana’ar goro ta kare haka ta katako, abin da ya rage mana a wannan gari shi ne hakar ma’adanai. Yanzu barazanar da muke samu a wannan sana’a ita ce ta neman kassara mu saboda a baya muna yin ta ce hankali kwance amma yanzu mun fara samu matsalar barayi ’yan garkuwa da mutane, baki ’yan China da ke neman kwace mana sana’a suna so su mayar da tarin al’ummarmu masu zaman banza, mu ne idanun gwamnati mu muke sawa ta gano inda ma’adanan suke a jibge, don haka ya kamata Gwamnatin Tarayya ta sanya ido ta dauki matakin kare al’ummarta da kasa baki daya,” inji shi.

ADVERTISEMENT

A jihohin Kurmi Jihar Osun na daya daga cikin jihohin da ke da tarin ma’adanan karkashin kasa da suka hada da zinare da sauran duwatsu masu daraja.