Search
Subscribe
Mahangar makekiyar makarantar Mama

Mahangar makekiyar makarantar Mama

Mahangar makekiyar makarantar Mama

Mahangar Mama

Matattarar mutane masu azama

Masu makama

Malumma

Masu kaimin kara himma

 

Batun babbaku da farfaru

Almajirai an taru

Malumma sun horu

Tarairayar biyayya ta gyaru

Murmurewar moruwarmu ta karu

 

A zo ai gangami

A daina guna-guni

Ko yi wa juna gani-gani

’Yan makaranta ai sansani

Turakar tarbiyyar lallami

 

Zayyanar zanen ajami

Aji-aji kolaye na da fahami

Jigidar damar janjami

Sai ai ta kwami

Karkashin kulawar malami

 

Manhaja

Harsuna na da lahaja

Ko karin ja-in-ja

Akwai na Hauren-Danja

Da masu dafdalar Haurubja

 

’Ya’yan marasa galihu

Tarairayesu su bar ihu

Ko da taro da ahu

Sanwarsu na bisa murhu

Sai su san an musu sulhu

 

Ruge-rugen rangada rubutu

Rumbun roro rututu

Rashin rahoton ribatattu

Rummacen ramar ragaitatu

Rumurmutsar romon rikirkitattu

 

Makekiyar makaranta

Koyon watsattsake

Fannonin fahimta a take

Farfajiyar ilimi a fafata

Juhala an ba ta rata

 

Kwalejin kalato kalamai

Dimbin dibgin dalibai

Kakkabe karbar kwabbai

Duga-dugin dogarawar dubbai

Mattarar masanan malamai

 

Arewatawa

Arawa

Auzinawa

Ana abubuwa

A ta alkintawa

 

Jam’in jama’a

Jan ragamar jami’a

Jahilci ya wahala

Jami’ai ba kasala

Sakarci a ce da shi a’a

 

Ilimi

Shi ne babban makami

Garkuwar mai mukami

Kar a debe tsammanin kaimi

An kusa daina jimami

 

Inna tai makarantar Baba

Dalibai ne kan gaba

A ilimantar da ’ya’yan Abba

Su kware a kiwon dabba

Lambun kayan marmari a dasa ayaba

 

Sudan

Sirdi sadidan

Sukuwar sunkutar  sumuni

Sunce sasarin sanayyar sani

Sansanin sana’a haka suddan

Katar

Karamar kasar da ta kayatar

Kulunboton kumbiya-kumbiya ta kaskantar

Kaikayin karajin kurar kuryar

Karfin karafan karar kasurar

 

Mama tai hadin gwiwa

Hannaye ne da yawa

Don baiwa dalibai damar tilawa

Karatu ne mai ban sha’awa

Fannonin fafatawar farantawa

 

Lallai a tuna

Lamura sun guduna

Wasu ma ba magana

Abin da a ke so ya wakana

A kafa shi cikin lumana

 

In ta zam abin nuni

Sai masu hannu da shuni

Ba sauran mai shu’uni

Sai falle shafukan wuni-wuni

Karkarewar asarar muradun karni

 

A watanin da suka wuccike suka falla a guje kafafen yada kwakwazo da na watsattsake keke-da-keke sun kattaba rahoton yadda Maman Haurobiya, Uwargidan Baban-burin-huriyya ta yunkuro da kudirin kafa MAKEKIYAR MAKARANTAR MAMA, koda yake dai an fasko cewa, MIKAKIYAR MAKARANTARTA, ai ta BABA ce. Kuma wani lamari da ke da daure kurungu tamau, shi ne, shin wannan MIKAKKIYAR MAKARANTA da za ta zamo karin sahu a JAM’IN JAMA’AR JAMI’O’IN Haurobiya, wai MAKARANSUWA ce ko kuwa ’ya’yan marasa galihu, musamman ALARAMMAN ALMAJIRAN AREWATAWA da gama-garin masu BOBO DA KWAMBON BOKOKO  za su halarci farfajiya su yi ninkaya a kogin ilimu?

Jami’an ASUSUN ILIMI da ke tukin alli da jan ragamar harkokin hada-hadar manhaja mara hajijiya a jami’o’in Haurobiya, suna cikin jerin wadanda suka fara fito-na-fito da kafa wannan farfajiyar koyon watsattsake da buda wagagen litattafai. Watakila dai Mama na son yi wa Jami’an Asusun ilimi KISISINAR KISHIYA ko FACAKAR FANCAL-FANCAL DIN FACALA, ta wata siga, wato ta kafa turaka turke turka-turkar jami’an jami’o’in, ta yadda ba za a kara jin labarin YAJI-GAUTA ba, ko wani tsallen badaken fafutikar neman hakki, don cika lalita da inganta harkokin koyi-ka-koyar.

Idan kuwa wannan ita ce manufar Jami’an Asusun ilimi, to ina kira da karajin murya kan lallai su wancakalar da wannan manufa ta su, don mu ga irin takun Mama wajen kafa fankaceciyar farfajiyar koyi-ka-koyar, ta yadda za a shawo kan  masu manufar KOYI-KA-KARKATAR. Sanin kowa ne dai a yau Arewatawan Haurobiya na fafatawa da masu Haramta Bobo da kwambon bokoko; ga Garkuwar gagara-kuwa; ga zaman dirshen din kashe fatari a tsakankanin ’yan bana hauya  da ke gararambar gadin layi, suna ta layi kamar masu laulayi.  Abin da ba ku sani ba, ta yiwu a manhajar makekiyar makaranta akwai yiwuwar an tsara dabarbarun warare sasarin da ke haifar wa al’umma tarnaki.

Batu na ingarman karafunan titin tarragon kwangirin layin dogo, mun yunkuro don ganin an kafa MIKAKKIYAR MAKEKIYAR MAKARANTAR MAMA da BABBAR BUKKAR BOKOKO BABA, musamman jin cewa akwai hannaye da yawa na hadin gwiwa, wato dai kasashen Sudan da ke da sirdi sadidan da kasar Katar, karamar kasar da ke da kayatarwa.

Babbar manufar darasin wannan mako duk bat a wuce ganin kafuwar BABBAR BUKKAR BOKOKO BABAN-BURIN-HURIYYA BA, ta yadda za mu ga su A’ISHATU FIL JAMI’A sun fatattaki masu LAULAYIN ALAYEN LAUYE-LAUYE ba, wadanda suka kawo wa kawancen HIJABI DA ILIMI tarnaki, mu ma sai mu yi musu BURKAR BOKOKO. Tun da ’yan makaranta na sane cewa, a darasinmu na A’ISHATU FIL JAMI’A cewa aka yi: A’isha ita ce a jami’a, wata rana yaumil Juma’a an yi batun E ko a’a; to ai sai mu yasar da ba’a; wannan likita ce, waccan malama ce.

Muna nan muna jiran Makekiyar makarantar Mama, musamman ma ganin cewa ai Uwargidan tsohon Shugaba kasar Haurobiya mai sunan AaBaCaDa ai ta kwata irin wannan, inda ta fara share fage daga kasar Niyyar-jari, watakila ma MAKEKIYAR MAKARANSUWA ce ta kafa mai rahusar farashi shi ya sa ake ta tururuwa zuwa birnin Maradi, ga shi ma an ce tana kokarin bude wani yanki na katafariyar makarantarta a kasar nan. Haurobiyawa mu yi murna da wadannan farfajiyoyin ilimi.

Fatanmu dai ka da a kafa wa Haurobiyawa Makaransuwa mai tsandarewar tsawwalar tsada, ta yadda kolo da titibiri ’ya’yan Alaramman almajiran Arewatawa za su iya kutsawa da kurungunsu, su yi kafa-da-kafada da gama-garin al’umma, tare da sauran ’ya’yan masu hannu da shuni.

 

* * *

Korafi

Ja-in-jar janjamin jimamin jarrabawar jan-bakin jan-bakin jami’o’i. Wani Direban alli da ke birnin Dabo inda ba a dabo ya koka kan yadda mahukunta a kasar Haurobiya suka bari aka haifar wa daliban da ke hankoron kutsa kurungunsu jami’a tarnaki.

Daga Malam Kamilu da ke Karamar Hukumar Gwale-gwalen na mujiya, birnin Dabo, Jihar Tunbin-giwa

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin