✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahauta sun nemi gwamnatin Legas ta dage lokacin fara yanka da na’ura

  Daga daya daga cikin shugabannin mahauta da ke mayankar Oko-Oba a Unguwar Agege, Alhaji Ado Garba Bichi ya bukaci gwamnatin Jihar Legas ta dage…

 

Daga

daya daga cikin shugabannin mahauta da ke mayankar Oko-Oba a Unguwar Agege, Alhaji Ado Garba Bichi ya bukaci gwamnatin Jihar Legas ta dage lokacin fara yanka dabbobi da na’ura da ta shirya fara amfani da shi daga 1 ga Janairun badi, domin ba mahautan jihar damar ilimantar da abokan huldarsu kan sabon tsarin.
Alhaji Ado Garba ya bayyana haka ne lokacin da suke tattaunawa da Aminiya inda ya ce lokacin ya yi kadan saboda suna bukatar sanar da abokan kasuwancinsu kan sabon tsarin, domin wasu suna jin labarin za a bar yanka da hannu suka fara kaurace wa mayankar suna ganin kamar zai keta haddin addininsu.
Ya bukaci gwamnati ta sa malamai a cikin al’amarin domin jama’a su fahimci yadda abin yake kuma ta tabbatar ba wata mayanka a wajen ta Oko-Oba wadda ita ce sananniya, idan ba haka jama’a na iya komawa ga wadanda ke waje da ke yanka da hannu.
Alhaji Ado Garba ya nemi gwamnati ta duba batun kwashe kayansu daga inda ake ajiye shanu domin yawancin mutanen da ke zaune da dabbobin suna kula da su ne. “Dabbobi ba kamar kayan shago ba ne da za a iya rufe a wuce ba da matsala ba, domin akwai lokacin da dabba za ta bukaci taimako idan ba mutum kusa tana iya mutuwa,” inji shi.
Ya ce muddin aka ce su bar wurin to akwai bukatar gwamnatin ta sama musu wurin da ba za su yi nisa da dabbobinsu ba, kuma ya zamo yana da tsaro.