✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahautan Gombe na bukatar mayanka ta zamani

Sana’ar Fawa ta shafi lafiyar al’umma a kowane mataki domin idan aka yi dubi da irin dabbobin da ake yankawa da kuma lafiyarsu da yadda…

Sana’ar Fawa ta shafi lafiyar al’umma a kowane mataki domin idan aka yi dubi da irin dabbobin da ake yankawa da kuma lafiyarsu da yadda ake yanka su a mahautar Gombe hakan ya sa akwai bukatar a dauki matakin gaggawa don samar da mayanka ta zamani a birnin.

Mayankar Gombe wadda a baya take Unguwar Yelanguruza, tsohon Gwamnan Jihar Alhaji Danjuma Goje ne ya dauke ta ya gina wata a kusa da Kasuwar Katako da tsarin mayanka ta zamani, amma ta rasa abubuwan aiki na zamani a cikinta inda hakan ya sa Aminiya ta ziyarci mayankar don ganin halin da take ciki, inda ta tarar da yadda ake yanka shanu a kasa jini yana kwarara babu wadataccen ruwa da ake wanke naman balle ya wanke jinin.

Aminiya ta lura cewa mayankar tana bukatar ruwa da wutar lantarki da  firizoji don adana nama saboda gudun lalacewarsa kafin a sayar da shi ga jama’a.

Da Aminiya take zantawa da Shugaban Kungiyar Mahauta ta Jihar Gombe, Alhaji Kabiru Bala, ya tabbatar da cea suna bukatar mayanka ta zamani domin kare lafiyar naman da ake yankawa, inda ya ce wajen da suke yanka dabbobin nasu bai da tsarin da ya dace.

Alhaji Kabiru Bala, ya ce ba iya kwaryar Gombe ne ake da bukatar mayanka ta zamani ba, sauran kananan hukumomin jihar ma ba su da mayanka ban da wasu kananan hukumomi hudu.

Binciken da Aminiya ta gudanar ya gano cewa kananan hukumomin Kaltungo da Shongom da Billiri ne suke da ginannuna mayanka da ’yar Majalisar Tarayya Hajiya Fatima Binta Bello, ta gina musu sai guda daya a garin Bajoga.

A mayankar ana da jami’an lafiya guda uku zuwa hudu da suke duba lafiyar dabbobi kafin a yanka, wanda ana bukatar su fi haka inji Kabiru Bala.

Sannan ya tabbatar da cewa suna fama da karancin wutar lantarki da ruwa inda  kullum sai sun kashe Naira dubu shida wajen sayen mai da suke sawa a janareta sannan su samu ruwa daga rijiyar burtsatsen da suke da ita, inda ya ce suna bukatar taimakon gwamnatin Jihar Gombe game da hakan.

Alhaji Kabiru Bala, ya ce sun rubuta wa gwamnati ba sau daya ba, ba sau biyu ba don neman taimako amma har yanzu ba labari. A banbagren yadda ake daukar naman kuwa daga kwatar zuwa wuraren sayarwa a cikin gari ana daukar su ne a babura ko babur mai kafa uku.

A hakan ya ce jami’an lafiya suna yawan yi musu magana amma da yake ba su da motoci ko yadda za a dauki naman ya wuce ta hakan ba yadda suka iya.

Alhaji Kabiru Bala, ya ce a kowace rana a mayankarsu suna yanka shanu sama da 60, amma akwai lokacin da suke yanka har 200 kananan dabbobi kuwa suna yanka kamar 400.

Sai ya yi kira ga gwamnati ta shigo lamarin ta taimaka musu domin suna da mambobi sama da dubu 10 kuma suna da katin zabe idan aka taimaka musu za su zabi wanda gwamnati take so a lokacin zabe.

Shugaban mahautan ya kuma yi karin haske kan masu yanka dabbobin sata da ba sa kaiwa kwata su yanka, ya ce ba mahautansu ba ne domin mahautansu a kwata suke yankawa duk wanda bai yanka a kwata ba ana hukunta shi.