✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai digirin da ke hada aikin jarida da tuyar kosai

Sunday Williams Omega, matashi ne da ke ba jama’a da dama sha’awa a birnin Maiduguri, sakamakon wani sabon al’amari da ya bullo da shi. A…

Sunday Williams Omega, matashi ne da ke ba jama’a da dama sha’awa a birnin Maiduguri, sakamakon wani sabon al’amari da ya bullo da shi.

A matsayinsa na matashi maji karfi, kuma mai takardar shaidar digiri, maimakon tsayawa ga aiki kadai sai ya fara sana’ar tuyar kosai a harabar Kungiyar ’Yan jarida ta Kasa  (NUJ) reshen Jihar Borno, sana’ar da mutane da dama ke ganin ta mata ce.

Duk da cewa matashin yana samun kalubale iri-iri daga jama’a, ya ce wannan bai sauya masa tunani ba. Wadansu na ganin wannan sana’a kamar zubar da mutuncinsa ne, don ba sana’a ce ta mata don haka ya bar musu kayansu.

Sai dai ya ce akwai masu kara masa karfin gwiwa, inda wadansu kuma a bangare daya suke kushewa, har ta kai ana ce masa “Dan daudu.”

Takaitaceen tarininsa

Sunday Williams Omega cewa, an haife shi ne a garin Maiduguri kuma ya yi makarantar firamare a Gwange 1. Daga nan ya shiga makarantar sakandare, inda bayan ya kammala ne ya samu gurbin karatu a Jami’ar Maiduguri, inda ya karanci Aikin Jarida (Mass Communications).

Ya yi ayyuka a wurare da dama da suka hada da Gidan Rediyon Tarayya (Peace FM Maiduguri), kafin ya zama cikakken ma’aikaci da Radio Pride FM da ke Gusau a Jihar Zamfara, sai Radio Nigeria Equity FM, Birnin Kebbi, kafin ya komo Kanem Radio (Unimaid Radio) da aiki.

Sunday Omega yana rera wakoki, kamar yadda yake aikin gabatarwa (MC) a wajen biki da tarurruka.

Lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a wurin tuyar kosansa, Sunday Williams ya bayyana yadda ya fara tuyar kosai. Ya ce yin hakan yana ganin zai taimaka wajen rage girman kai a tsakanin matasa.

Dalilin fara sana’ar tuyar kosai

“Akwai dalilai guda uku da suka sa na fara wannan sana’a ta tuyar kosai. Na san darajarta, domin da ita aka dauki nauyin rayuwata har na girma.

“Haka kuma wannan sana’a gadonta na yi, domin tun muna yara na tashi na ga mahaifiyata tana tuyar kosai, duk da yanzu ta tsufa ta daina. Sannan da wannan sana’a na yi karatu tun daga firamare har zuwa jami’a kuma har waka ina yi.
“Shi kansa kosai, har waka na yi masa a kan yadda ya taimaki rayuwata.

Daya daga cikin ma’aikatan Williams mai kosai

“Sai abu na biyu, na dauki wannan sana’ar ce don in koya wa matasa cewa kada su raina sana’a komai kankantarta.

Matsalar matasanmu na yanzu suna raina sana’a ko idan an ga kai kana yi a rika yi maka kallon raini. Don haka kada ka ce wai ka yi karatu, kana jiran gwamnati ta ba ka aiki,” inji shi.

Ya ci gaba da cewa, “Ka ga akwai ire-irena wadanda suna aikin albashi, sai kuma su ki kama wata sana’a. Suna zaman majalisa amma ka ga na kama sana’a don fadakar da matasa su guji raina sana’a. Hakan ya sa na fara wannan sana’a kuma sai godiya ga Allah.

“Abu na uku, duk abin da mutum yake yi yana yi ne don ya samu wani abu na kudin shiga, wanda da a ce na fara wannan sana’ar tun da dadewa, da a yanzu ban san inda Allah Ya kai ni ba.”

Sunday ya kara da cewa duk da ya yi karatun digiri, bai ga dalilin da zai sa ya kyamaci karamar sana’a ba.

Ya sha suka daga mutane

“Ko a lokacin da zan fara wannan sana’a, sai da na dauki hotuna na sa a shafina na Facebook amma idan ka ga irin maganganun da mutane suka yi, sai ka yi mamaki.

“Kai wadansu har zagi sun yi, sun ce ni dan daudu ne. Wadansu kuma suka yaba, domin sana’a ce da za ta taimaka sosai.

“To ka ga idan da za a fadakar da matasa kan muhimmancin sana’a, matasanmu ba za su yi zaman kashe wando ba.

“Kuma a yadda na san matasanmu, bari mu fada wa kanmu gaskiya, ya kamata mu ajiye girman kai, mu kama sana’a komai kankantarta.

“Alal misali, Hausawa sai ka ga mutum da bakar goro yana tallar goro ko dabino amma idan ka ji abin da yake samu a sana’ar sai ka yi mamaki. Ka ga ashe raina sana’a ba ya da kyau” inji matashin dan jarida mai tuyar kosai.