Da Dumi Dumi

Mai duka ya kawo mana dauki

Sakonni:

Assalamu alaikum , Bayan gaisuwa tare da fatan alherin mai duka  a gare mu daliban makarantar mu mai albarka ta malam DODO uban Dodanni, tare  da fatan zaku zo gana ba tare da gangamin hotiho ba. Wajen yadda shagabanninmu suke gana kyankyashe a hannun mu , saboda haka yaku ‘yan uwana mu mu an fanu da uwar jin mu da dukiyarmu,kwakwalen mu don kwakulo abin da zai fishe mu, da bada lokaci muhimmanci wajen yin addu’o’i akan neman zaman lumana a kasar mu ta Haurobiya . da mu zama masu fadar alkairi ko mu yi shiru.
Daga Saka-ka-taren Jihar Yawon-Bebe, Abubakar Charismatic 07037865413.

Ta’aziyya
Assalamu alaikum ya ‘yan uwana ‘yan makarantar dodordo da ke bude wagawaga shafin amintattar jaridar da ake bugawa a babban birnin Haurobiya. Muna sanar da dalibai na rashin yayan mahaifin shagaban Jahar Mu-muka-fara Shari’a  a makwanin da suka arce Mai-duka ya yi masa rahama amin. Ahmad Hashim Pedo shagaban Jihar Mu-muka-fara Shari’a  08065749945.

Ta’aziyya
Assalamu alaikum ya ‘yan uwana ‘yan makarantar Dodorido da ke bude wagawaga shafin amintattar jaridar da ake bugawa a babban birnin Haurobiya. Muna sanar da dalibai na rashin Baffan Aisha Haifa Mataimakiyar jami’in hulda da jama’a ta kasa a makonin da suka arce, Mai-duka ya yi masa rahama  ya kai ga makwancinsa amin.
Daga Aisha Haifa Mataimakiyar jami’in hulda da jama’a ta kasa, a Jihar Bayan kada 08068026431.

ADVERTISEMENT

Yaudarar kai
Sallama irin ta masu kallon alkibla sau babban lauje a duk rana ku, jinjina ga mata masu bada himma wajen bada kulawa da shawarwari a wannan shafi mai albarka na Dodorido .A wannan makon zan yi sharhi ne a game da abin da yake faruwa a cikin ‘yan uwana masu daura zannuwa da daura dankwali, yanzu daura dankwali ya zama kwali kon in ce kurun kus domin ba duka mata ke son daura dankwali don mutunta kai ba. Na yi nazari yawa-yawan mata sun dauki yaudara da karya, bin masu zama a kan buzu marasa tsoron Mai-duka  sukan zama buzuzu idan dare ya yi dare kuwa ya zama nama, ga yin ‘yar manne da juna, wa iya zi billah mai duka ya kawo mana dauki, ga kuma wuce raini. Idan nace yaudara da mata ke yi itace yanzu-yanzu za su nuna suna yi da kai, to amma da zarar sun sami wanda ya fika abin hannu sai su yi zilliya da zagayeyeniya ba iwa irin su kawayen su zilla-ziyya dasu zayyana tunda sun lakanci zayyanawa mutum abu dalla-dalla kamar a cikin dala. Karya kuma ai ado ce idan bakyayi kauce ki bamu wuri ko kuma ki wuri-wuri da na mujiya, mun yi sai kizo kawalliya, da zarar sun kyalla na mujiya sun ganki da sutura fes-fes ko kina rike wani katon kurtun Magana to sun fara fesa ta kamar far feso da fetsarwa  ba kakkautawa mai duka ya rabamu da masu karya. Idan ana Magana ta dan mannau tsakakin mace da mace abin sai na ce wa iya zibillah mai duka ya gyara, a kasar nan tamu ta gado ta Haurobiya idan jama’a za su je gidan Malam Tunau a ka mika dokar daura na tantabara tsakanin jinsi ka ji tabarbarewar rayuwa. ‘yan uwana mata mu ki yaye idan mace ba ta bada kanta ga da na miji to ai ba zai mata dole ba ko ba haka ‘yan uwana mata?. Mu guji irin wadannan dabi’u domin aminta ba raki wurin Mai-duka.

Daga dalibar Jihar dakin kara, Zarah 081397888991.

Share