Search
Subscribe
Mai gadi ya yi wa ‘yar shekara 10 fyade da naira 20

An kama tsohon soja saboda zargin fyade

Mai gadi ya yi wa ‘yar shekara 10 fyade da naira 20

Kotun majistare a Minna ta bayar da umarnin tsare wani mai aikin gadi Michael Itang dan shekara 55 a gidan yari saboda zargin yi wa ‘yar shekara 10 fyade.

Kotun dai na tuhumar Itang ne akan laifin yi wa karamar yarinya fyade.

Dan sandan da ya shigar da karar ASP Daniel Ikwoche, ya bayyana wa kotun cewa, wata da ta kawo wa ‘yan sandan karar mai suna Grace Tanko wacce take zaune a kusa da babban asibitin Suleja, inda ta sanar wa ofishin ‘yan sandan karamar hukumar Suleja jihar Neja ranar 3 ga Oktoba 2018 abinda Itang ya aikata.

Ana dai zargin wanda ya aikata fyaden da baiwa yarinyar kudi tsakanin naira 20 zuwa naira 100 kafin ya aikata laifin.

Alkalin kotun majistaren Nasiru Muazu ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare mai laifin a gidan yari har zuwa ranar 25 ga Oktoba 2018  don ci gaba da sauraran karar.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin