Da Dumi Dumi

Mai hakar kabari da ke sayar da kokon kan mutum Naira 6000 ya shiga hannu

Wadanda ake zargi da hada-hadar koqunan kan mutane
Wadanda ake zargi da hada-hadar koqunan kan mutane

Wani mai aikin hakar kabari a makabartar Unguwar Oke Sunna a Legas ya shiga hannu bayan da aka yi zargin ya cire kokunnan kan mutane a makabartar yana sayar wa matsafa a kan Naira dubu shida kowane guda.

Wanda ake zargin mai suna Kazim Olarewaju ya ce shekara biyu ya shafe yana aikin haka kabari a makabartar amma sau biyu kadai ya taba sayar da kokon kan mutum inda a karo na farko ya sayar da guda biyu kan Naira dubu 12 yayin da asirinsa ya tonu  lokacin da ya yi yunkurin yin haka a karo na biyu.

Ya ce ya fara harkar ce bayan da ya hadu da wani mai sayar da maganin gargajiya mai suna Murtala Salami wanda suka hadu da shi a makabartar lokacin da ya je domin binne wat ’yar uwarsa. Ya ce a lokacin Murtala ya same shi a gefe ya ce yana bukatar ya ba shi biskit sai ya ce bai gane me yake nufi ba. Sai ya ce masa yana nufin kokon kan mutum inda da farko ya turje ya ce ba zai yiwu ba amma daga baya ya amince.

Bayan wani lokaci ya ba shi Naira dubu 12 na kokon kai biyu, daga baya ya kuma bukata, sai dai a lokacin da ya yi yunkurin kai masa ne sai ’yan sanda suka kama shi.

Mai maganin gargajiyar Murtala Salami ya ce yana amfani da kokon kan mutum ne domin maganin kasuwa, inda y ace yana dakawa ne ya mayar da shi gari inda yake barbadawa a ruwan magani yana sha da safe kafin ya ci abinci. Ya ce a baya kafin ya hada maganin yakan yi cinikin Naira dubu 30 a kowace rana amma bayan ya da ya fara amfani da maganin yakan yi cinikin Naira dubu 80 zuwa dubu 100 a kullu.

ADVERTISEMENT

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Legas DSP Bala Elkana ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce suna bincike kafin a gabatar da wadanda ake zargin a kotu domin su fuskanci shari’a.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya