✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai hidimar kasa ya rasa hannunsa daya da ya rage

Wani mai yin hidimar kasa mai suna Nuruddeen Tahir dan asalin Jihar Kano da aka tura Jihar Taraba wanda bayan an ba su horo jami’an…

Wani mai yin hidimar kasa mai suna Nuruddeen Tahir dan asalin Jihar Kano da aka tura Jihar Taraba wanda bayan an ba su horo jami’an hukumar suka nemi ya koma jiharsa ta asali ya yi hidimar kasar saboda tausaya masa ganin hannunsa daya, amma ya zabi zama a jihar ya rasa daya hannun a wani hadarin mota da ya rutsa da shi.

Kamar yadda wakilinmu ya binciko, Nuruddeen ya rasa hannunsa daya ne tun yana karami amma wannan bai hana shi neman ilimi ba, har ya kai ga ya samu digiri a Jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano.

Shugabar Hukumar Masu yi wa Kasa Hidima ta Jihar Taraba Madam Florence Yahatua ta ce bayan kammala horar da masu yi wa kasa hidimar an tausaya wa Nuruddeen Tahir sabo da kasancewarsa mai hannu daya aka ce ya koma jiharsa ta Kano ya gudanar da aikin yi wa kasa hidimar amma ya ce rashin hannu daya ba zai hana shi zama ya yi wannan aiki a Jihar Taraba ba.

Ta ce Nuruddeen din ne ya nemi a kai shi yankin tsaunin Mambilla da ke Karamar Hukumar Sardauna sai kuma ga shi ya gamu da hadari tare da wadansu ’yan uwansa masu yi wa kasa hidima su 17 inda daya daga cikinsu ya rasa ransa.

Madam Floerence ta ce sauran sun sami raunuka amma Nuruddeen hannunsa daya da ya saura ne ya guntule inda hakan ya sa a yanzu ba ya da hannu ko daya.

Ta ce wannan hadari ya gigita hukumar yi wa kasa hidima a jihar. Kuma ta nuna godiyarta ga shugaban hukumar yi wa kasa hidima ta kasa Birgediya-Janar Shu’aibu Ibrahim saboda irin taimakawar da ya yi tare da ganin wadanda suka gamu da hadarin sun samu kula ta musamman.

Madam Florence ta kuma yaba wa shugaban hukumar kan alkawarin da ya yi na sama wa Nurudden hannayen roba wadanda za su taimaka masa ya iya rubutu da cin abinci tare da sauran wasu abubuwa.

Ta nuna takaicinta kan yadda wadansu suka soma neman kudi wai da nufin za su taimaka wajen jinyar Nuruddeen inda ta ce ba a neman ko sisin kwabo daga kowa don yi wa Nuruddeen jinya. Ta ce masu neman kudin karya suke yi suna neman su damfari ’yan Najeriya ne kawai domin hukumar yi wa kasa hidima ta dauki nauyin

jinya tare da sama wa Nuruddeen hannayen roba.

Madam Florenece ta yaba wa Gwamnan Jihar Taraba Mista Darius Ishaku saboda nuna damuwarsa kan wannan hadari da ya rutsa da matasa masu yi wa kasa hidima a jihar.

Kuma ta gode wa Shugaban Cibiyar Lafita ta Tarayya da ke Jalingo, Dokta Inusa Wiza saboda kulawa mai kyau da ake bai wa Nuruddeen da sauran wadanda suka samu hadarin.