✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai kamfanin takalma na neman miliyan 500 daga Drogba

Wani attajiri da ya mallaki wani kamfanin yin takalma a kasar Kanada, Jordan Pascals ya yi karar shahararren dan kwallon Kwaddebuwar nan Didier Drogba a…

Wani attajiri da ya mallaki wani kamfanin yin takalma a kasar Kanada, Jordan Pascals ya yi karar shahararren dan kwallon Kwaddebuwar nan Didier Drogba a gaban wata kotu da ke Amurka don tilasta masa ya biya  tarar Fam miliyan 1 da dubu 25 (kimanin Naira miliyan 500).

Jordan Pascal ya ce yana neman kotun ta tilasta Drogba ya biya shi kudin ne sakamakon saba alkawarin da ya yi a wata yarjejeniya da suka kulla a  shekarar 2017 inda aka shirya Drogba zai halarci wani bikin tallata kayayyakin kamfaninsa na Jordan Pascal’s Ludury Brand JAD a birnin Landan, amma dan kwallon ya ki halarta ba tare da wata hujja ba.

Jordan Pascal ya ce:  “Wannan abu da Drogba ya yi, ya zubar mini da kamfanina mutunci, inda na rasa da yawa daga cikin masu hulda da ni, na yi asarar makudan kudi, kuma kamfanin ya shiga tangal-tangal saboda matsalar rashin kudi.”

Mista Pascal ya ce abin da Drogba ya yi ya saba wa dokar yarjejeniyar kuma hakan ya jawo wa kamfaninsa JAD mummanar faduwa da rasa dimbin masu hulda da shi, inda wadansu suka dauki kamfanin a matsayin mayaudari kuma maci amana.

Jaridar The Sun ta Ingila ta ce yunkurin da Pascal ya yi na ganin Drogba ya mayar masa da kudin kwantaragin da suka kulla ya ci tura, tun yana bi a hankali har tura ta kai bango inda ya yanke shawarar kai dan kwallon kotu.

A watan Nuwamban bara ne Drogba ya yi ritaya daga buga kwallon kafa bayan ya kammala kwantaragin shekara 1 da kulob din Phoenid Rising Stars da ke Amurka.

Ya yi suna a lokacin da ya buga wa kulob din Chelsea kwallo inda ya samu nasarar lashe kofuna da dama ciki har da na Zakarun Turai a shekarar 2012.

Drogba yana daga cikin tsofaffin ’yan kwallon da kulob din Chelsea ya gayyata a wani wasan sada zumunta da za a yi amfani da kudin wajen tallafa wa marasa galihu. Wasan zai gudana ne a filin wasa na Chelsea a tsakanin kulob din Chelsea da zababbun ’yan kwallon Ingila a ranar 16 ga watan Yuni mai zuwa.

Rahotanni sun ce Drogba yana fata kotun za ta yi watsi da karar a zamanta na farko saboda bai yarda da zargin da attajirin yake yi masa na kin cika alkawari ba.

Yanzu haka Drogba yana da shekara 41 kuma ya mallaki wani kulob a Amurka inda ya kasance dan Afirka na farko da ya mallaki wani kulob a tarihin Amurka.