✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai Martaba Sarkin Tambuwal Ya rasu

Allah Ya yi wa Mai Martaba Sarkin Tambuwal Alhaji Mainasara Sa’ad Dahiru Tambuwal rasuwa. Ya rasu da dare a ranar Alhamis 13 ga watan Agusta…

Allah Ya yi wa Mai Martaba Sarkin Tambuwal Alhaji Mainasara Sa’ad Dahiru Tambuwal rasuwa.

Ya rasu da dare a ranar Alhamis 13 ga watan Agusta 2020 a Abuja bayan shafe tsawon lokaci yana fama da rashin lafiya.

A yau Jumu’a ake sa ran za a yi jana’izarsa.

Ana kuma sa ran a Karamar Hukumar Tambuwal ne za a yi masa sallah.