✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai musayar kudi ya mutu da lambar sirrin masu ajiya Naira biliyan 50

Mutumin da ya bude cibiyar hada-hada da musayar kudade  ta KuadrigaCD’s  mai suna Gerald Cotten, mai shekara 30, wanda kuma shi kadai ne ke da…

Mutumin da ya bude cibiyar hada-hada da musayar kudade  ta KuadrigaCD’s  mai suna Gerald Cotten, mai shekara 30, wanda kuma shi kadai ne ke da kalmar sirrin gano kudaden abokan hulda ya rasu yayin da matarsa ke fuskantar baraza a tsakaninta da wadanda suka mallaki kudaden.

Kamfanin musayar kudade na cryptocurrency da ke kasar Kanada ya ce, ba zai iya biyan kudaden da suka  kai Fam miliyan 110 (kimanin Naira biliyan 50 da miliyan 652 da dubu 150 ga abokan hulda ba, saboda wanda yake da lambar sirrin ma’ajiyar kudaden ya mutu, shi ke da kalmar sirrin gano bayanan abokan huldar.

Gerald Cotton ya rasu ne sanadiyyar wata cuta mai crohns da ke damunsa a ciki a lokacin da ya tafi kasar Indiya don bude gidan marayu a watan Disamba. Kamar yadda matarsa Jennifer Robertson ta sanar.

Jennifer Robertson ta ce, mijinta ne kadai zai iya gano asusun kudaden da ake magana, babu wani ma’aikacin kamfanin da ya san lambar sirrin ma’ajiyar kudaden, matar ta bayyana haka ne a takardar rantsuwa da ta rattaba wa hannu a matsayin kariya ga wanda za a tuhuma da karbar kudade a ranar 31 ga Janairu.

Misis Robertson ta ce, kudaden abokan hulda da ke hannun kamfanin sun kai Naira biliyan 50 da miliyan 652 da dubu 150, Mista Gerald ne kadai yake da lambar mabudin ajiyar kudaden, ba sauran ma’aikatan kamfanin ba.

Misis Robertson ta binciki kwamfutar mijinta amma ta gaza bude kalmar sirrin da za ta gano bayanan abokan huldar da suka adana kudaden a kamfanin, hakan y asa ta dauki hayar masanin Kwamfuta don bankado kalmar sirrin da mijinta yake amfani da ita wajen gano bayanan kudaden abokan hulda na kamfanin duk da haka ba a yi nasara ba, kamar yadda ta bayyana wa kotun.

A ranar 3 ga Janairu 2019 daraktocin kamfanin suka nemi shaidar kariya daga karbar bashi don ci gaba da tuhumar da ake yi wa kamfanin.

A cikin jawabin daraktocin sun ce, mako guda ke nan suna ta kokari a kan hanyoyin da za su warware matsalar da ke tsakaninsu da abokan hulda, ta hanyar tuntubar cibiyoyin kudade da bankuna don amincewa da kwafin takardar karbar kudade da aka bai wa kamfanin. Kuma an samu nasarar shirin da ake yi.

Abokan huldar Kamfanin KuadrigaCD na ta bayyana korafinsu a shafukan sadarwa na zamani cewa, ba su iya cire kudadensu daga asusun ajiyarsu.

Daya daga cikin abokan huldar kamfanin Ally Shapobal ya rubuta sakon cewa, mako biyu da suka wuce ya cire kudi daga asusun ajiyarsa, “Ina kudina yake yanzu? Ban ga sauran kudina ba. Na tura sakon imel amma ba a turo min amsa ba,” inji shi.

Wadansu abokan huldar na dada tambaya cewa, Gerald Cotton ya mutu amma wadansu ma’aikatan kamfanin na yi masu karya a kan mutuwar.