Mai shekara 27 da ya yi wa wata mai shekara 38 fyade ya shiga hannu

Wani matashi mai suna Adam Kunle mai shekara 27 da ake zargi da ya yi wa wata wata mata mai shekaru 38 fyade ya shiga komar ‘yan sandan jihar Ogun.

Kakakin Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun DSP Abimbola Oyeyemi, ya shaidawa Aminiya cewa matar da matashin ya yi wa fyaden wacce aka sakaye sunan ta, ita ta shigar da kara a ofishin Rundunar da ke yankin Ibafo, inda ta shaida cewa tana kwance a dakinta da misalin karfe 12 na rana matashin da ke zaune a wani gida da ke daura da gidan da take ya sadada ya shiga dakin nata inda ya sadu da ita ta karfin tsiya.

Ya ce, wanda ake zargin ya amsa laifin sa, ” Ya shaida mana cewa, ya dade yana neman matar da badala inda taki amince masa, shi ne ya yi amfani da wannan dama ya mata fyade a lokacin da ya fuskanci ita kadai ce a gidan.”

DSP Abimbola Oyeyemi, ya kara da cewa matashin zai fuskanci shari’a yayin da aka garzaya da matar asibiti domin kula da lafiyarta.

ADVERTISEMENT
Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya