Da Dumi Dumi

Mai shekara 37 ta haifi ’ya’ya 38

Wata mata mai shekara 37 ’yar kasar Uganda ta haifi ’ya’ya 38, inda ta ta samu tagwaye shida da ’yan uku sau hudu da ’yan hudu sau uku, ta kuma haifi ’ya’ya daidaiku sau biyu, bayan da aka aurar da ita tana da shekara 12 ta haihu bayan shekara guda. Matar mai suna Mariam Nabatanzi Babirye tana zaune ne a kauyen Kabimbiri da ke gundumar Mukuno a Uganda.

Mazauna kauyen matar da ke yawan haihuwa sun yi mata lakabi da “uwar tagwaye mai haihuwa ’yan hudu.” Al’amarin wannan mata ya zama abin mamaki ganin yadda ta samu haihuwar tagwaye shida da ’yan uku sau hudu da ’yan hudu sau uku, ta kuma haifi ’ya’ya daidaiku sau biyu. Duk da ana ganin cewa yawan hayayyafa alheri ne, amma ba haka lamarin yake game da Mariam, wadda ta ce a zuri’arsu an samu irin yawan haihuwa, kamar yadda ta bayyana wa wata jaridar kasar Uganda Daily Monitor. 

“Mahaifina ya haifi ’ya’ya 45 da mata daban-daban kuma duk sun fito ne a matsayin ’yan hudu,” inji ta.

Mariam dai an ce ba ta yi dacen miji ba, domin ba ya taimaka mata, kuma kananan ’ya’yansa ma ba su san shi ba, saboda rashin zama.  

ADVERTISEMENT

“’Yan uwanmu ba su san kamannun mahaifinmu ba. Ni ma na saba ganinsa ne lokacin ina dan shekara 13, kuma da daddare kawai muke haduwa, don ba ya dadewa yake tafiyarsa,” a cewar Charles Musisi babban dan Mariam mai shekara 23.

Mariam ta shawarci iyaye das u daina sayar da ’yta’yansu da sunan auren wuri. Sannan ta bukaci maza su rika kula da matansu.

Likita Dokta Kiggundu ya ce ba a taim aka wa Mariam ba, da an ba ta shawarar abin da ya dace ta yi. Domin likitoci na iya tsayar da haihuwar ta hanyar toshe mahaifarta.

Da jaridar Daily Nation ta bayyana labarin wannan mata, sai mutane suka tara mata kudi don tallafa mata wajen ilimantar da ’ya’yanta. A rahoton jartidar kasar Tanzania The Citizen, an tara mata kudin da ya kai kudin kasa R136,500, tun sa’adda aka sanar da halin da take ciki a watan  Afirilun bana.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya