✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai shekara 60 ya kwana 4 yana watangaririya a teku ba abinci

Wani tsoho mai suna John Low mai shekara 60 daga kasar Singapore da ke tukin kwalekwale ya shafe kwana hudu yana watangaririya a cikin tekun…

Wani tsoho mai suna John Low mai shekara 60 daga kasar Singapore da ke tukin kwalekwale ya shafe kwana hudu yana watangaririya a cikin tekun Kudancin China sanye da rigar ceto, bayan kwalekwalensa ya kife a cikin tekun.

A ranar 4 ga Mayu ne, John Low, ya shirya don yin hutunsa a Tsibirin Tekun Tioman da ke Kudancin China, a nan ne igiyar ruwa ta kifar da kwalekwalensa yayin da shi kuma ya fada a cikin tekun.

Kafin ya farga har ruwa ya fara shiga cikin kwalekwalen wanda hakan ya sa kwalekwalen ya fara nutsewa a cikin ruwan. John dai sai ya yi fara dabarar ta amfani da rigar kariya da ke bayansa don gudun kada ya nutse saboda ba zai iya yin ninkaya don ya fita daga cikin tekun zuwa gabar ruwa ba.

Ya yi kokarin fita daga cikin tekun, amma abin ya ci tura tun daga karfe 10 na daren ranar da kwalekwalen ya nutse bai iya ganin karshen ruwan tekun ba, sai ya fara shiga cikin wani mayuyacin hali, har zuwa kwana hudu yana rayuwa shi kadai ba tare da abinci ko ruwan sha ba.

John Low, ya bayyana wa jaridar China ta Lianhe Zaobao irin rayuwar da ya yi a cikin tekun na tsawon kwana hudu ba ci ba sha. Ya ce hakan sai dai kawai ruwan gishiri da yake iya gani idan dare kuma ya yi bai iya ganin komai.

Akwai lokacin da John ya yi nasarar amfani da wata na’ura da ke nuna alamar mutum yana cikin mayuyacin hali “bro”  da ke jikin agogon hannunsa kirar Roled.

Wannan na’urar mutum na iya amfani da ita ce idan yana cikin damuwa. A hoton farkon da ya dauka bayan an kubutar da shi daga cikin tekun ya nuna yadda fatar jikinsa ta bushe tare da yin saba. John, ya bayyana wa manema labarai cewa, ya cire kayan jikinsa ne bayan ya fahimci cewa, kayan na mannewa da fatar jikinsa, hakan ya sa bai bukatar hasken rana.

“Idan har na daga kaina sama, zan fara jin alamar kamar fuskata na konewa tare da jin zafi mai radadi,” inji shi.

Ya ce, “Idan har ina son kauce wa jin wannan zafin sai dai kawai in rika sanya fuskata a cikin ruwa, saboda ina cikin ruwa na tsawon kwana hudu, idan har na saka fuskata a cikin ruwa ina jin kamar ana tsikarina da allurai dubu ne. Don haka ya zama min dole ko dai in hakura da radadin hasken rana ko kuma na ruwa.

Bayan wadannan  kwanaki a cikin ruwan gishiri, wasu sassan jikinsa sun rika yi masa ciwo.

Tsohon mai shekara 60, ya ce a lokacin da ya fara ganin abubuwa tare da sauraren murya, sai ya dakatar da na’urar ya ci gaba da jure wa zafin jikin da ke damunsa, ba don kansa ba sai don iyalansa.

Daren na hudu da ya zamar wa John, ranar da zai kubuta daga cikin tekun wani jirgin ruwa mai suna Diogo Cao, ya zo wucewa ta inda yake sai nau’urar buoy ta sanar wa jirgin cewa akwai alamar mutum a wurin. Hakan ya sa ma’aikatan jirgin ruwan suka ceto shi.  John, ya ce abin da zai iya tunawa shi ne, “Na kubuta, yanzu zan iya yin barci.”

Bayan kubutar da John Low, ya yi kwana biyu yana jinya a asibiti a Singapore da kuma ganin likita na kwana shida.

Likitocin asibitin, sun ce John yana fama da cutar huhu kuma kodarsa ta mutu sadoda rashin isashshen  ruwa a jiki tare da kuna a duk jikinsa.

John,  a yanzu haka ya samu sauki kuma ya ziyarci ma’aikatan jirgin ruwan Diogo Cao don gode musu a kan ceton rayuwarsa da suka yi.

John Low, ya kara da cewa, “Ina fata ba wani mutum da ya makale da yake neman agajinku.”

Cikin murna ya fada wa wadanda suka ceto shi bayan ya rungume su.