✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai shekara 74 ta haifi ’yan biyu

Wata mata mai shekara 74 mai suna Mangayamma  da ke Kudancin Jihar Anthar Pradesh a kasar Indiya ta haifi ’yan biyu mata. Matar wanda take…

Wata mata mai shekara 74 mai suna Mangayamma  da ke Kudancin Jihar Anthar Pradesh a kasar Indiya ta haifi ’yan biyu mata.

Matar wanda take tare da mijinta mai suna Yaramati Sitarama Rajarao, wani manomi a kauyen Nelaparthipudi suna zaman aure  tun 1962, kuma ma’auratan sun kai shekara 54 amma babu haihuwa a tsakaninsu.

Likitoci ne suka karbi haihuwar ’yan biyun wanda aka yi nasarar yi mata dashensu a mahaifarta.

Likitan matar, Dokta Umar Sankar ya fada wa sashen Telugu na BBC Landan cewa matar da jariran suna cikin koshin lafiya.

Mai jegon, Mangayamma Yaramati, ta ce ita da mijinta mai shekara 82 sun dade suna neman haihuwa amma kuma ba su samu ba sai a wannan lokaci.

Mijinta, Sitarama Rajarao, shi ma ya fada wa BBC jim kadan da haihuwar ’yan biyun cewa suna cike da farin ciki mara misaltuwa.

Sai dai kuma kwana daya tsakani, Mista Rajarao ya samu matsalar mutuwar barayin jiki inda a yanzu yake samun kulawa a asibiti.

“Ba mu da ikon yin komai, duk abin da zai faru, ba makawa zai faru. Komai yana hannun Ubangiji,” inji Mista Rajarao lokacin da aka tambaye shi kan ko wa zai kula da jariran idan ta Allah ta kasance a kansu lura da tsufarsu da yanayin shekarunsu.

Samun magada abu ne mai muhimmanci ga ma’auratan da suka ce ana nuna musu wariyar launin fata a kauyensu sakamakon tsawon lokacin da aka dauka ba tare da sun haihu ba.

Yaramati, ta ce sau da dama mutane kan fada mata magana kan rashin samun haihuwa. Ta ce, mun yi iya yinmu sannan mun ga likitoci daban-daban amma wannan rana ita ce rana mafi farin ciki a rayuwata.

An dai haifi ’yan biyun ta hanyar yi wa mahaifiyarsu tiyata, hanyar da aka fi amfani da ita a irin yanayin da mahaifiyarsu take ciki.

A shekarar 2016 ma wata mata ’yar kasar Indiya mai shekara 70, mai suna Daljinder Kaur ta haifi santalelen da, inji BBC.