Da Dumi Dumi

Mai shekara 83 ya yi digiri na biyu

Wani tsoho mazaunin kauyen Daata da ke yankin Hoshiarpur,  a kasar Indiya mai suna Sohan Singh Gill, ya ajiye karatunsa ne bayan kammala Kwalejin Khalsa a garin Mahilpur a  1957, amma sai ga shi  ya fara karatun koyon malanta a kwalejin Khalsa a birnin Amritsar da ke kasar Indiya.                                                                                                                                                Bayan samun digiri na biyu yana da shekara 83, Sohan Singh Gill ya nuna cewa tsufa bai hana neman ilimi. Ya samu kwarin gwiwa mai yawa daga wajen jama’a da dama bayan samun wannan digiri a jami’ar Jalandhar da ke kasar Indiya.

Sohan ya ce, “Mataimakin Shugaban Makarantar Sakandaren da ya kammala mai suna Waryam Singh ne ya ba ni shawarar ci gaba da karatun saboda in zama malamin jami’a, kuma  na amince da shawarar ganin ina da sha’awar haka, sai na koma kasar Kenya a Nahiyar Afirka na samu aikin koyarwa a jami’a. Na dawo Indiya a 1991 har zuwa 2017, na koyar a makarantu da dama, amma a koyaushe burina in samu digiri na biyu.”

Shekara biyu da suka gabata ya yi rajistar karatun harshen Ingilshi a jami’a sannan ya shiga Jami’ar Karatu Daga Gida.

Sohan, ya kara da cewa, “Da taimakon Allah, burina ya cika a karshe, darasin harshen Ingilishi ya kasance abin da na fi sha’awa tun ina da kuruciya. Zamana a kasar Kenya ya taimaka min samun wannan digiri.

“Na kasance ina samun kyakkyawan sakamakon jarrabawa lokacin da na koma makaranta, don haka na fara tunanin zan iya cimma burina,” inji shi.

ADVERTISEMENT

An haifi Sohan a ranar 15 ga Agustan 1937 kuma ya yi makarantar firamarensa a mahaifarsa sannan ya wuce makarantar sakandaren Khalsa a Mahilpur, ya kuma kasance shahararre a fannin wasan kwallon kafa. Bayan komawar Sohan Kenya ya ci gaba da sha’awar wasan da yake da shi. A cewar Sohan rayuwar da yake cikin koshin lafiya ne ya samu nasarar cika burinsa.

Sohan ya ce, “Bayan burina ya cika a yanzu haka ina sha’awar rubuta litattafai don yara.”

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya