✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mailafiya ya yi amai ya lashe kan Boko Haram

Ya ce a kasuwar kauye aka gaya masa cewa wani gwamna ne shugaban Boko Haram

Tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Obadiah Mailafiya ya janye kalaman da yi game zaman wani gwamna a Arewacin Najeriya shugaban kungiyar Boko Haram a Najeriya.

 

Mailafiya wanda ke karin haske game da zargin da ya yi wanda ya bar baya da kura, ya ce ya samu bayanan da ya yi ne a hirarsa da wasu Fulani a kasuwar kauyensu a lokacin da ya je sayen acca.

A wata hira da ya yi da wani gidan radiyo, ya yi ikirarin kasancewa daga cikin wadanda suka tattauna da tsoffin kwmandojin Boko Haram da suka tuba.

Ya kuma hakikance cewa shi shaida ne, kuma tsoffin mayakan sun gaya musu cewa wani gwamna mai ci a Arewa ne Kwamandan kungiyar.

A lokacin hirar, ya ce bakin Boko Haram da ‘yan bindigar da ke addabar yankin Arewa maso Yamma daya ne, kuma sun bazu a sassan Najeriya inda nan gaba za su rika kai wa manyan mutane hari a birane suna kashe su.

Mailafiya wanda kalaman nasa suka sa hukumar tsaro ta DSS yi masa tambayoyi na sa’a bakwai tare da kira daga kungiyar gwamnonin Arewa da a yi cikakken bincike domin gano gaskiya ya janye zargin daga baya.

Janye zargin ya zo ne bayan Shugagan Kungiyar Gwamnonin Arewa, Gwamna Simom Lalong na Jihar Filato a cikin wata sanarwa ya ce zargin ya fi kawar a kawar da kai daga gareshi, dole a bincika.

Mailafiya ya kuma bayar da hakuri ga duk wadanda kalaman nasa suka saba wa, yana mai cewa ba da nufin tayar da fitina ya yi ba.

Hirar tasa wadda a ciki ya yi zargin cewa Boko Haram da ‘yan bindiga na shirin fara yakin basasa a shekara ta 2022 ta karade shafukan zumunta tare da haifar da muhawara.

A ranar Alhamis hukumar kula da kafafen watsa labarai (NBC) ta ci tarar gidan radiyo na Nigeria Info Naira miliyan biyar saboda hirar.

NBC ta ci tarar ne saboda gidan radiyon ya bari Mailafiya ya yi amfani da kafarsa wajen yada zarge-zargen da ba za a iya tabbatarwa ba da kuma kulaman batanci.

Amma a wata hira da aka yi da shi daga baya, Mailafiya ya ce ya yi bayanan ne saboda damuwarsa da matsalolin da suka addabi yankin Arewa da kasa baki daya.

Ya ce bai taba tunanin hirar tasa game da matsalolin tsaro a Arewacin Najeriya da Kudancin Kaduna za ta yi yawo haka ba.

A hirarsa da BBC Hausa ya ce a iya saninsa ya yi hirar ce da wani gidan radiyo da bai sani ba a Jihar Legas, amma ba da saninsa suka nada ba.

“Na dauka wani karamin gidan radiyo ne a Legas” inji shi.

Ya ce shi cikakken masoyin Shugaba Buhari ne da kuma Arewacin Najeriya inda matsalar tsaro ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.