Daily Trust Aminiya - Mailantarki ya sha da kyar a fadan APC da PDP
Subscribe

Mailantarki ya sha da kyar a fadan APC da PDP

A ranar Juma’ar da ta gabata ce wakilin mazabar Gombe da Kwami da Funakaye a Majalisar Tarayya, Alhaji Khamisu Ahmed Mailantarki, ya tsallake rijiya da baya a yayin da wasu matasa suka nemi tozarta shi a lokacin daurin auren ’yar tsohon Kwamishinan Kudi na Jihar Gombe Alhaji Inuwa Yahaya Umaru a kofar Fadar Gombe.
Wannan lamari ya faru ne a lokacin da matasan APC da na PDP suka fara kai ruwa rana bayan da magoya bayan Jam’iyyar APC suke rika cewa sai Buhari wanda hakan ya tada husumar da aka raunata wasu mutum biyu.
Wani da abin ya faru a idonsa (da ya bukaci a sakaye sunansa) ya bayyana wa wakilinmu cewa a lokacin daurin auren magoya bayan jam’iyyun biyu sun fara jifar juna da bakaken kalamai da hakan ya sa suka harzuka har ya ja hankalin jami’an tsaro suka tarwatsa su.
Majiyar ta ce matasan PDP ne suka fara jifar na APC da duwatsu da kai musu sara da miyagun makamai.
Ganin ya sha da kyar, Khamisu Mailantarki, bai iya tsayawa a Gombe don ganawa da mutanensa ba,  nan take ya tafi Bauchi.
A bangare guda wani taron dinke ’ya’yan Jam’iyyar APC da aka shirya ya kare cikin rudani, inda wasu ‘ya’yan jam’iyyar suka zargi Mailantarki da cewa yana so ya yi amfani da damar wajen saye ’ya’yan jam’iyyar.
Abdullahi Kabo, ya shaida wa wakilinmu cewa Mataimakiyar Shugabar Mata ta jam’iyyar Hajiya Amina ce ta kira taron da sanin shi Mailantarki kuma yana wurin da taron ya gudana da nufin ya sa jam’iyyar a aljihunsa.
Abdullahi, ya zargi Mailantarkin da kawo wasu mutane daga Gombe ta Kudu suka maye gurbin wasu daga Gombe ta Arewa a lokacin taron don ya samu biyan bukatarsa.
Da manema labarai suka tuntubi Mailantarki, ta bakin tsohon Shugaban Jam’iyyar CPC na Jihar Barista Audu Baba Kwami, ya ce duk dan jaridar da yake son jin ta bangarensu ya bi su zuwa Bauchi inda ya ce a can ne zai iya gaya musu duk abin da suke so su ji.

texem
More Stories