✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa na zargin FIRS da kin karbar harajin N1.4bn

Rashin cire wasu kudi na haraji daga ma'aikatu da hukumomin gwamnati ya jawo wa FIRS tuhuma daga majalisa.

Majalisar Dattawa na zargin Hukumar Tara Haraji ta Kasa (FIRS) da kin sanya N1.4bn na harajin ta ta karba daga ma’aikatu da hukumomi (MDAs) a asusun Gwamnatin Tarayya.

Tuhumar na kunshe ne a rahoton binciken shekarar 2015-2020 da Babban Oditan Tarayyar ya gabatar wa Kwamitin majalisar kan asusun gwamnati wanda Sanata Mathew Urhoghide ke jagoranta. 

“An bukaci Shugaban FIRS da a cire WHT din da ba a cire ba na N700.2 miliyan daga kasafin MDAs da abin ya shafa kamar dokar FIRS ta 2007 ta tanadar.

Rahoton ya ce an ciri kudaden da kasafin hukumomin amma ba a tura wa FIRS ba.

Hakan ya karya dokar kudi mai lamba 234 (III), ga duk jami’an da suka kasa cire harajin VAT da WHT, kuma za a  sanya musu takunkumi a karkashin dokar VAT mai lamba 102 na 1993 wacce ta hada da tara ko dauri.

Ya kara da cewa za su shawarci Ankata Janar na kasa a kan a cire kudaden daga cikin kasafin karkashin sashi na 24 na dokar FIRS.

Rahoton ya kuma ce an cire N708.5m na kudin haraji daga ma’aikatu da hukumomin gwamnati 31 amma ba a tura wa FIRS a rubuce ba.