✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa ta amince da dokar hana bara a Kano

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta zartar da kudurin dokar hana bara ta shekarar 2013 a fadin jihar bayan da dokar ta samu goyon baya daga…

Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso na Jihar KanoMajalisar Dokokin Jihar Kano ta zartar da kudurin dokar hana bara ta shekarar 2013 a fadin jihar bayan da dokar ta samu goyon baya daga ’yan majalisar lokacin da akawun majalisar Malam Lawan Badamasi ya yi mata karatu na farko da na biyu da na uku. Aminiya ta rawaito cewa jim kadan da kammala karatun dokar a zagaye na uku ne, Mataimakin Shugaban Majalisar Alhaji Isyaku Ali Danja wanda ya shugabancin zaman majalisar ya ce da zarar dokar ta fara aiki, to yawon bara ya haramta a jihar. A lokacin da yake yi wa Aminiya karin haske game da dokar, shugaban masu rinjaye na majalisar Injiniya Hamisu Ibrahim Cidari daga karamar Hukumar Makoda, ya ce an tanadi hukuncin daurin wata biyu ko kuma biyan tarar Naira dubu biyar ga duk wanda kotu ta samu ya karya dokar. Ya ce kafin a amince da dokar gwamnatin Jihar Kano ta kakkafa cibiyoyi a dukan kananan hukumomin jihar inda aka umarci mabarata kowa ya je garinsu ya yi rajista don samun tallafi daga gwamnati, ya ce gwamnati tana so ta kyautata rayuwar almajirai fiye da abin da suke samu a wurin bara.
’Yan majalisa da suka hada da Alhaji Muhammad Isa daga karamar Hukumar Tarauni da Alhaji Garba Idu daga Tsanyawa da Alhaji Abdullahi Iliyasu Yaryasa daga Tudun Wada, sun ce dokar za ta zama karbabbiya kuma ta zama mai amfani ga yaran da ake kawowa cikin birni daga wurare daban-daban da niyyar almajirci.