✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa ta amince da Naira dubu 30 mafi karancin albashi

A yau Talata majalisar dattawa ta amince da Naira dubu 30 a matsayin mafi karancin albashin ma’aikatan gwamnatin tarayya da na jihohin Najeriya. Amincewar ta…

A yau Talata majalisar dattawa ta amince da Naira dubu 30 a matsayin mafi karancin albashin ma’aikatan gwamnatin tarayya da na jihohin Najeriya.

Amincewar ta biyo bayan rahoton kwamitin wucin gadi da majalisar ta kaddamar wanda mataimakin mai tsawatarwa na majalisar yake jagoranta Francis Alimekhena.

A watan Janairun 2019 ne zauren majalisar wakilan tarayyar Najeriya suma suka amince da Naira dubu 30 a matsayin mafi karancin albashi.