✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa ta amince wa gwamnati ciwo bashin Dala bilyan 22

A ranar Alhamis din makon jiya ne Majalisar Dattawa, ta amince wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ciwo bashin Dala biliyan 22. Hakanya biyo bayan…

A ranar Alhamis din makon jiya ne Majalisar Dattawa, ta amince wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ciwo bashin Dala biliyan 22.

Hakanya biyo bayan shawarar da Kwamitin Majalisar Dattawa Mai lura da Basukan Cikin Gida da Waje ne ya bayar.

Shugaban Kwamitin, Sanata Clifford Ordia na Jam’iyyar PDP daga Jihar Edo, ya karanto rahoton kwamitin, inda  ya nemi Majalisar Dattawan ta amince a ciwo bashin.

Sai dai kuma bukatar a tattauna batun ba tare da ’yan jarida ba, ta haifar da cece-ku-ce a tsakanin wakilan majalisar da har tsawon fiye da minti 30.

Shugaban Masu Rinjaye,  Sanata Abdullahi Yahaya da Shugaban Marasa Rinjaye, Sanata Enyinnaya Abaribe, sun bada shawarar a fito a yi wa majalisar bayani dalla-dala kan batun da karbo bashin ya kunsa.

An ci gaba da tafka muhawara da musayar yawu har sai da Shugaban Majalisar ya tsawatar. Bayan an dan yi shiru na minti biyar kuma an tuntubi juna, sai Sanata Yahaya ya nemi a yi bayanin a asirce, sannan aka amince.

Tun cikin watan Nuwamban bara ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya mika wa majalisa yana neman amincewarta ya ciwo bashin Dala biliyan 22 domin gudanar da ayyukan raya kasa.

Tuntuni ya kamata a ce an yi wasu ayyukan raya kasa a tsakanin shekarar 2016 zuwa 2018, amma ba a yi ba saboda karancin kudaden shiga.

Shugaba Buhari ya aika wa majalisar a zamanin Sanata Bukola Saraki yana neman amincewa a ciwo bashin Dala bilyan 30, amma ta ki amincewa.

Tsohon Sanata Shehu Sani ya ce sun ki amincewa da a ciwo bashin a wancan lokacin ne domin hana Najeriya ruftawa cikin ramin matsalar tattalin arzikin da ba ta iya fitowa idan bashi ya yi mata katutu.

A halin da ake ciki dai a yanzu, kudaden da Najeriya ke samu a duk wata masu dimbin yawa na tafiya ne wajen biyan bashin da Gwamnatin Tarayya ke ciyowa.